Shafin Farko

Sulaimanu Ɗan Abuhama 1807 – 1819 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Sulaimanu shi ne sarki na arba’in da huɗu a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na farko a cikin zuriyar Fulani. A farkon sarautarsa Fulani sun hana shi shiga gidan Rumfa, saboda haka sai ya zauna a gidan Sarkin Dawaki. Yana nan zaune cikin wannan gida sai wani mutum ya ce da shi, “Idan baka shiga gidan Rumfa ba Kanawa ba za su bika ba”. Da ya ji haka sai ya aikewa Fulani cewa yana nemansu. Su kuma suka amsa masa da cewa, “Ba za mu zo wurinka ba, sai dai kai ka zo wurinmu duk da cewa kai ne sarki. Idan ka je gidan Malam Jibir ma zo gare ka”. Ya tashi ya je kuma ya kira su suka amsa.

Da suka taru sai ya tambaye su, “Don me kuka hana ni shiga gidan Rumfa?” Sai Malam Jibir ya ce da shi, “Don kada mu shiga gidajensu mu haifi ‘ya’ya su koma ga halayensu”. Da sarki ya ji haka sai ya ƙyale su ya tafi zuwa ga Shehu Usmanu ya nemi izin shi kuma ya bashi takobi, da wuƙa da tuta, ya kuma yardar masa ya shiga gidan Rumfa. Sa’annan ya shiga ya kuma samu ikon Kanawa birni da ƙauye aka bishi. Sarki Sulaimanu ya mulki Kano tsawon shekara goma kafin ya mutu.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.