Shafin Farko

Tukur Ɗan Ballo 1893 – 1894 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Tukur shi ne sarki na arba’in da tara a jerin sarakunan Kano. Sannan kuma sarki na shida a jerin sarakunan Fulani.

Sarki Tukur bai samu goyon bayan jama’a ba wajen naɗinsa. Ya shiga gidan sarauta ta Ƙofar Fatalwa. Ya kai kimanin kwanaki goma sha a cikin rumfar kara da ya yi a gidan sarauta ba tare da an zo an yi masa caffa ba.


Rumfar Kara

Sai daga baya wasu ‘yan tsiraru da suka haɗa da Wamban Kano Shehu, da Mamman Mai Lafiya, da Galadima Yusufu da wasu ‘yan mutane kaɗan suka yi masa caffa.

Bayan fitowar Galadima Yusufu daga gidan sarki sai mutane suke yi musu ba’a da cewa, “Mutum biyar sun rinjayi mutum ɗari”.

Bayan Galadima Yusuf ya yiwa sarki Tukur caffa an yi masa waccar ba'a, sai abun ya ɓata masa rai, saboda haka suka taru shi da sauran ‘ya’yan sarki gidansa da ke Ciranci, suka yanke shawarar cewa su fice su bar garin. Sun fita ta Ƙofar Nassarawa inda suka tsaya suka kwana da safe suka rankaya zuwa Wudil, daga nan sai Kademi, sai suka zarce zuwa Takai, inda suka je suka yi shirin yaƙi sannan suka koma Kano, suka fara yaƙi har sai da suka kai Ƙofar Mata gindin rimi. Da sarkin Gaya Dabo ya samu labari, sai ya ɗaura ɗamarar yaƙi ya je ya fatattake su. Jama’a suka bisu da ihu suna zaton sun gudu ne ashe sun sake komawa Takai ne suka sake sabon shirin yaƙi.

 
An kashe sarki Tukur a garin Tafashiya da ke kusa da garin Ɗanzabuwa.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.