Shafin Farko

Usmanu Ɗan Dabo 1846 – 1855 Miladiyya


Gabatarwa

Usmanu Ɗan Dabo shi ne sarki na arba’in da shida a jerin sarakunan Kano sannan kuma sarki na uku a jerin sarakunan Fulani.

Kalmar nan ta “Mai Babban Ɗaki” ta samo asali ne a zamaninsa, saboda ya ginawa mahaifiyar babban gida Tafasa sai aka riƙa kiranta wannan laƙabin.
A lokacinsa ya samu kangara daga Haɗeja. Sannan kuma a zamaninsa Sarkin Dutse Bello ya kangare sai aka hilace shi aka tuɓe shi. Haka nan kuma shi ne sarkin day a gina a Gogel, saboda yana da gona a can. Ya mulki Kano tsawon shekara ɗaya da wata goma.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.