Shafin Farko

Yaji Ɗan Daɗi 1753 – 1768 M


Gabatarwa

Sarki Yaji Ɗan Daɗi shi ne sarki na arba’in a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Maryam. Sarki Yaji Ɗan Daɗi sarki ne mai adalci da nagarta. Saboda wannan dalili ne ma ya sa matansa suke kiransa da “Malam Lafiya”. Iya tsawon mulkinsa ƙasar Kano ta zauna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ba yaƙe-yaƙe, ba takurawa. An samu yawaitar mutane masu yin hijira zuwa birnin Kano a zamaninsa. Har ya yi sarauta tsawon shekara goma sha biyar da wata goma Kano bata taɓa yaƙi ba.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.