Shafin Farko

Kanajeji ɗan Yaji 1390 – 1410 Miladiyya


Gabatarwa

Kanajeji shi ne sarki na goma sha uku a jerin sarakunan Kano. Asalin sunasa shi ne Ibrahim. Sunan mahaifiyarsa Aunaku. Sarki Kanajeji ya kasance mutum mai fitina, tunda ya hau karagar mulki bai zauna a gida ba. Shi ne sarki da ya yaƙi ƙasar Zazzau. Sarki ua haɗa rundunar mayaƙa da kayan abinci aka haɗu a Turunku. Kamar yadda ya zo a littafin Labarun Hausawa da Maƙwabtansu. Amma Gwangwazo (2005) ya ce a Kudan aka fafata. A koma dai ina aka fafata wannan yaƙi, rudunar mayaƙan Kano basu samu nasarar wannan yaƙi ba. Wannan hart a saka sarkin Zazzau alfahari yake cewa: “Wane abu ne Kanawan Kanajeji ye?”.

Bayan dawowar sarki da jama’arsa gida da ƙyar, sarki ya fara neman yadda za a samu galaba a kan Zazzagawa. Sai ɗaya daga cikin ragowar waɗanɗan kafirai ya bashi shawarar cewa ya rungumi gunki, abinda kakaninsa da iyayensa suka tozarta. Haka kuwa aka yi, Sarki ya bi shawarar Bamaguje. Sai ya tambaye shi “Sanar da ni abinda zan aikata”. Sai ya ce das hi, “Ka yanki wannan reshen wannan itaciya (Itaciyar da gunkin Tsimbirbira ya taɓa zama)”, ya yanki reshenta, ya taras da macijiya ja a cikin reshen, ya kashe ta ya sami fatarta ya ɗinka huffi biyu da ita. Kuma ya sassaƙa dundufa huɗu da kuntukuru takwas da reshen itaciyar. Ya ɗauka zuwa Ɗanƙwai ya jefa su a cikin ruwa. Ya komo zuwa gidansa ya zauna kwana arba’in, sannan ya koma ya ɗauko su, ya kawo gidan sarkin Cibiri. Sarkin Cibiri ya ɗinke su da ragowar fatar macijiyar nan, y ace wa Kanajeji, “Idan kana son kowane abu daga na al’amarin duniya sai ka aikta abin da kakaninmu suka aikata tun da”. Ya ce, “To, sanar da ni, na yi”. Sarkin Cibiri ya tuɓe rigarsa ya ɗaura huffin fatar macijiyar nan, ya gewaya itaciyar nan sau arba’in yana waƙa irin waƙar Barbushe. Haka kuma Kanajeji ya yi.

Bayan afkuwar wannan da shekara ta kewayo, sai sarki Kanajeji ya fita zuwa Zazzau, ya zauna a Gadas kamar yadda aka wallafa a klittafin Labarun Hausawa da Maƙwabtansu. Sai dai, Gwamgwazo (2005) ya bayyana cewa bayan waccar ridda (fita daga Musulunci da sarki Kanajeji ya yi saboda amincewarsa da aikata abin da sarkin Cibiri ya umarce shin a tsafi), daga baya ya tuba ga Allah. Kuma koma cikakken Musulmi. Sannan kuma yaƙin ma a Shika aka fafata shi. Kuma a wajen yaƙinma shi sarki Ibrahim Kanajeji ya karanta wannan ayar y ace, “Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai, sau da yawa Allah yakan bai wa jama’a kaɗan galaba a kan jama’a mai yawa da ikonsa. Allah yana tare da masu haƙuri”.

Bayan da sarkin Kano Ibrahim ya bada umarni rundunarsa suka afka cikin rundunar sarkin Zazzau Muhammadu Abu, guri ya kaure, yaƙi ya kai matuƙa.  A wannan yaƙi a shekara ta 1399 aka kashe sarkin Zazzau, aka tarwatsa rundunarsa. Aka kamawa na kamawa, daga baya sarkin Kano Kanajeji ya zauna a wannan gari na shika har tsawon watanni bakwai ko kuma shekara ɗaya cur a wata ruywara. Wannan ta saka ake yi masa kirari: “Bakano kere, Kanajeji masharuwan Shika, hana wankan Kubanni, make-make garin magabata”. Ya yi sarautar Kano ta tsawon shekaru ishirin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.