Kofar Barbushe

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Barbushe 1124M


Gabatarwa

Ƙofa ce da aka gina ta a kusa da gidan Wazirin Kano. Sunan wanna ƙofa ya samo asali ne daga Barbushe jikan Dala. Wannan da ya taɓa zama shugaban masu bautar Tsimbirbira. Wannan ƙofa yanzu babu ita.

Sunnan wannan ƙofa ya canja daga Ƙofar Barbushe zuwa Ƙofar Bai a cikin shekarar 1425, kuma a lokacin sarkin Kano Dauda. Wannan kuma ya faru ne lokacin da wanni hakimin Borno mai suna Dagaci ya ƙaura Kano sakamakon saɓani da suka samu da sarkinsa. Shi wannan mutum Dagaci ya kai wa sarki caffa. Da zai koma masaukinsa da ke gunduwawa, sai sarki ya yi masa rakiya har wannan ƙofa ta Barbushe, ta nan ya fita. Saboda haka sai sarki Dauda ya ce a riƙa kiran wannan ƙofa da sunan wannan Dagaci.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub