Kano Ƙofar Ɗan'agundi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kano Ƙofar Ɗan'agundi 1472M


Gabatarwa


Kano Ƙofar Ɗan'agundi

An gina wannan ƙofa zamanin sarkin Kano Muhammadu Rumfa. Bayan an kammala gina wannan ƙofa sai sarki ya saka mata suna ƙofar Kudu. Bayan shekara huɗu da gina wannan ƙofa sai aka samu wata mata Bakanuwa ta zo yamma da wannan ƙofa daga cikin birni ta kafa bukka ta sauka a ciki ta riƙa sana’ar sayar da rogo.

Lokacin da wannan mata ta zo wannan guri tana da ciki. Kwanci-tashi wannan mata ta haifi ɗa namiji ta kuma saka masa suna Kokau. Ana-nan ana-nan, sai Kokau ya girma a wannan guri. Sai kuma ya fara yiwa mutane fashi. Idan mutane za su shiga ko za su fita sai ya tare su ya ce sai sun bashi kayansu. Ana nan sai mutane suka fara ƙorafi da cewa, kai bana son bi ta wannan ƙofar saboda ɗanbanzar yaron nan Ɗan’agundi. Da haka-da-haka wannan suna ya bi wannan ƙofa har yau ɗin nan. Shi kuma Kokau yana cikin aiwatar da wannan mummunar sana’a tasa wata rana sai ya je ya yiwa wasu matasa majiya ƙarfi fashi suka kashe shi kowa ya huta.

Manazarta:


Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da Ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa (Sunan gurin ɗab'i ya yage daga jikin littafin da aka nazarta).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub