Kofar Nassarawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Kawaye/Ƙofar Nasarawa, Kano 1466


Gabatarwa

Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya gina wannan ƙofa, a cikin aikinsa da ya yi na faɗaɗa birnin Kano, amma tun can asali akwai wata ƙofar mai irin wannan sunan da sarki Gijimasu ya gina a daidai ƙofar Gidan Ɗan’iya Aminu. To da sarki Muhammadu Rumfa ya tashi aikin faɗaɗa gari, sai ya rushe wannan ƙofa ya matso da ita gurin da Ƙofar Nasarawa take a yanzu. Sannan ya sake maida mata wancan suna na Ƙofar Kawaye. Wannan suna na Kawaye sunan wata matar Gyarta Wasa ce.

Sarki Abdullahi ɗan Dabo shi ya canja sunan wannan ƙofa daga Ƙofar Kawaye ta Koma Ƙofar Nasarawa bayan hawansa kujerar mulki da shekaru goma sha ɗaya. Ya zo a ruyawa cewa sarki Abdullahi ya fita kilisa wata rana sai ya yi yankin Magwan, yana zuwa kudu da wannan dutse na Magwan, sai ya nuna wani guri ya kuma bayar da umarnin a gina masa gida a wannan waje. Da aka kammala gina gida aka zuba kayan alatu a ciki. Sai sarki ya saka rana ya je ya buɗe wannan gida. Sannan kuma ya shiga masallaci aka yi sallar Azahar a wannan gida. Da ya kammala sai ya yiwa wannan gida laƙabi da “Gidan Nasarawa”. Wannan gida yana nan a kan titin “State Road”. Bayan kammala dukkan abubuwan da zai yi, sai kuma da zai koma gida ya biyo ta wannan ƙofa, da ya zo daidai wannan ƙofa sai ya ja linzami ya sauka, sannan ya umarci liman aka yi addu’a aka shafa, ana kammala wannan addu’a sai ya sake cewa, “A riƙa kiran wannan ƙofa da sunan Ƙofar Nasarawa”. Wannan abu ya faru a shekarar 1866 Miladiyya (Gwangwazo, 2003, Ƙwalli, 1996).

Wannan ƙofa ta Nasarawa ta samu sabuntawa har sau biyu. Na ƙarshe kamar yadda yake a wannan hoto, an yi shi ne zamanin Gwamnatin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso. A shekarar 2015.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub