Kofar Alasan

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sabuwar Ƙofar Alasan, Kano 937M


Gabatarwa

An gina wannan ƙofa a zamanin sarki Abdullahi Bayero. Sunanta ya samo asali ne daga tsohon attajirin nan wato Alasan Ɗantata. Bayan haka kuma mutane suna kiranta da Ƙofar Dole, saboda dole ce ta sa aka huda ganuwa aka samar da ita sakamakon ruwa da ya ke taruwa a wajen kuma yana yawan rusa garu. Sannan kuma ana kiranta da ƙofar mayanka saboda ta yi kusa da mayanka.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub