Kofar Wambai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Wambai, Kano (1118)


Gabatarwa

Wannan ƙofa ta Wambai an gina ta ne a shekarar 1118 Miladiyya. Ta samu canje-canjen sunaye daga sunanta na asali. Sunan wannan ƙofa na asali shi ne Ƙofar Adama. Wannan suna ya samo asali ne daga sunan mijin jikar Dala; wato maharbin da ya fara zama a kan Dutsen Dala. Daga cikin ‘ya’yan Dala akwai wani mai suna Gagiwa, shi kuma Gagiwa baban Hanga ne, ita kuma Hanga ita ce matar Adama.

Bayan shekaru 300 da gina wannan ƙofa, a zamanin sarki Daudu kamar yadda Daneji (1425), ya kawo, an yi wani baƙon hakimi mai suna Digaci wanda ya taso daga Borno, sakamakon savani da ya shiga tsakaninsa da Sarkin Borno na wancan zamanin. Da ya iso Kano sai ya sauka a Jigirya wanda yanzu ake kiranta da ‘Yankaba. Bayan Digaci ya huta gajiyarsa, sai ya kai gaisuwa zuwa fadar sarki. Da zai shigo birnin Kano sai ya shigo ta wannan ƙofa ta Adama, shi da jama’arsa. Haka nan kuma ma da ya tashi fita sai ya fita ta wannan ƙofa. An ce ma sarki da kansa ya raka shi har zuwa ƙofar. Saboda wannan dalili sai sarki Daudu ɗan Kaneji ya canzawa wannan Ƙofa suna ta tashi daga Ƙofar Adama ta koma Ƙofar Dagaci.

Sannan kuma a lokacin Sarkin Kano Muhammadu Nazaki, wannan ƙofa ta tashi daga sunan Ƙofar Dagaci ta koma Ƙofar Wambai, wanda da shi ake kiranta har zuwa yau ɗin nan. Dalilin haka kuwa shi ne cewa shi sarki Muhammadu Nazaki yana da wani ɗa da ya yiwa sarautar Wamban Kano. Bayan yiwa wannan ɗa nasa sarauta sai kuma ya gina masa gida a kusa da wannan ƙofa ta Dagaci. Shi wanann ɗan sarki ya kasance mai ɗaukaka ne da kuma yawan jama’a. Saboda wannan ɗaukaka tasa kuma ga gidansa daf da wannan ƙofa sai ya zama mutane da kansu suna kiran wannan ƙofa da Ƙofar Wambai. Da haka wannan suna ya bita. Wannan al’amari ya faru a shekarar 1620.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub