Abinci Mai Gina Jiki

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abinci Mai Gina Jiki


Gabatarwa

Akwai wasu sinadaran abinci waɗanda jiki ke buƙata don ya yi aikin da ya kamace shi, sannan kuma ya kasance cikin ƙoshin lafiya. Abin so ne ya zama a duk lokacin da za a ci abinci, ya zama ya ƙunshi waɗannan sinadarai. Abincin da ya tattaro waɗannan sinadarai a kwano ɗaya, shi ake kira abinci mai gina jiki.

Wannan rubutu da za a karanta zai yi ƙarin haske ne game da shi ainihin abinci mai gina jiki. Menene ko wannene abinci mai gina jiki? Daga waɗanne irin nau’ukan abinci ake samunsa, sannan kuma meye amfaninsa ga ɗan’adam?

Abinci Mai Gina Jiki

Abin da ake nufi da abinci mai gina jiki a wannan rubutu shi ne abin da aka kira “Balanced Diet” a Turance. Masana wannan fanni, kamar Krans (2016), sun fassara shi a matsayin ‘Abincin da ke baiwa jiki sinadaran da yake buƙata ya yi aiki kamar yadda ya kamata’.

Wato kenan, abinci mai gina jiki shi ne dukkan abincin da ya tattaro nau’ukan sinadaran abinci guda biyar da suka haɗa da: Kabohaidiret (carbohydrate), bitamin (Vitamins), maiƙo (fats), furotin (protein), da kuma minarals (minerals). Ƙari a kan wannan shi ne samun shan isasshen ruwa.   

Amfanin Abinci Mai Gina Jiki

Babban amfanin abinci mai gina jiki shi ne tabbatar da lafiyar jiki da kuma bashi kuzari. Ta wannan hanya jiki ke samun garkuwa wacce ke bashi kariya daga saurin kamuwa da cututtuka, da kuma bashi damar aiwatar da dukkan ayyukan da suka da ce da shi.

Ƙungiyar lafiya ta duniya (World Health Organization), ta faɗi cewa, cin abinci mai gina jiki yana bada kariya daga kamuwa da dukkan nau’ukan cututtukan ƙarancin abinci (malnutrition) da kuma cututtuka marasa yaɗuwa kamar irinsu ciwon siga (diabetes), ciwon zuciya (heart disease), ciwon shanyewar jiki (stroke), ciwon daji (cancer), da saursansu.

Kenan, mai karatu zai iya yaƙar waɗannan cututtuka da aka lissafa a sama da ma wasunsu ta hanyar abinci. Abin yi kawai shi ne, a faɗaɗa bincike.

Illar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

Ƙarancin abinci mai gina jiki na da illoli da dama, daga cikinsu akwai barazanar kamuwa da cututtukan da suka haɗa da; cutar kansa, ciwon zuciya, ciwon sikari, saurin gajiya, da sauransu (Kumar, 2012; Krans, 2016; who, 2015), duk sun yarda da wannan.

Hanyoyin Samun Abinci Mai Gina Jiki

Ana samun waɗannan sinadaran abinci mai gina jiki daga naukan abincin da suka haɗa da bitamin (Vitamins), furotins (proteins), kabohaidiret (carbohydrate), maiƙo (fat), sai kuma kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa (fruits & vegetables).


Kayan Marmari (fruits)

Mazarta:


Krans B. (2016). Balanced Diet. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.healthline.com/health/balanced-diet#Overview1

Chefstevamalta (2016). The Importance of Balanced Diet. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.chefstevemalta.com/importance-of-balanced-diet.html

Kumar P. (2012). Balanced Diet and Its Components. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http:// www. nutritionist- resource.org.uk/articles/balanced-diet.html

World Health Organization (2011). What is the recommended food for children in their very early years? An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.who.int/features/qa/57/en/.

World Health Organization (2015). Healthy diet. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.who.int/mediacentre/factsheets/fs394/en/


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub