Abincin Hausawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abincin HausawaGabatarwa

Kamar yadda aka san kowace ƙabila tana da nau’ukan abinci (cimaka) nata na asali, to haka ma Hausawa. A tare da haka kuma, ba a rasa wasu nau’ukan abincin da wasu jama’a suka zo daga baya suka kuɗe cikin wannan al’ummar. A wannan rubutu, za mu rubuto nau’ukan abincin gargajiyar Hausawa da kuma waɗanda daga baya (lokaci mai tsawo) suka gauraya suka zama na Hausawa.

Tare da haka za mu karkasa wannan abinci zuwa nau’uka huɗu: Abinci, miya, abin sha da kuma kayan ƙwalam-da-maƙulashe.

Abubuwan Ci

 1. Ɗanwake, wanda ya karkasu zuwa:
  • Ɗanwake.
  • Ɗanwaken fulawa.
  • Gudun ƙurna/Ɗanwaken alkama.
  • Tubani/Soto.
 2. Tuwo, shima yana da yawa. Daga ciki akwai:
  • Tuwon biski.
  • Tuwon dawa; ana yi da gero ko dawa da sauran dangoginsu.
  • Tuwon laushi.
  • Tuwon tsari; ana yi da gero ko dawa da sauransu. Amma an fi yi da gero.
  • Tuwon kanwa; ana yi da gero ko dawa da sauransu.
  • Tuwon shinkafa.
  • Tuwon masara.
  • Tuwon fulawa da sauransu.
 3. Gurasa, abincin Larabawa ce daga baya ta zama ta Bahaushe musamman Bakane.
 4. Waina, tana da nau’uka biyu:
  • ‘Yar tsala ko ‘yar tsame: Ana jefa ta cikin ruwan mai a soya.
  • ‘Yar tanda, ita ce wainar da ake soya ta da tanda. Ita bata shan mai sosai.
 5. Ƙosai.
 6. Dambu.
 7. Fate-fate.
 8. Kwaɗo:
  Kwaɗon gayan tuwo.
 9. Kwaɗon dankali. Kwaɗon rama Kwaɗon zogale. Da sauransu.
 10. Wasa-wasa.
 11. Samɓara.
 12. Alkubus, abincin Larabawa ne daga baya ya zama na Hausawa.
 13. Sinasir. Abincin Larabawa ne daga baya ya zama na Hausawa.
 14. Finkaso.
 15. Dashishi.

Abubuwan Sha

 1. Kunu. Yana da na’uka kamar haka:
  • Kunun tsamiya.
  • Kunun gyaɗa.
  • Kunun zaƙi.
  • Kunun aya.
  • Kunun kanwa.
  • Kunun ɗinya, da sauransu.
 2. Fura, asali abincin Fulani ce.

Miya

 1. Miyar kuka.
 2. Miyar zogale.
 3. Miyar kuɓewa.
 4. Miyar dage-dage.
 5. Miyar taushe.
 6. Miyar gyaɗa.
 7. Miyar yakuwa.
 8. Miyar albasa.
 9. Miyar karkashi
 10. Miyar lalo.
 11. Miyar ayoyo.
 12. Miyar shuwaka.

Kayan Ƙwalam-da-Maƙulashe

Wasu lokutan kuma akan ce kayan tanɗe-tanɗe da lashe-lashe.

 1. Alkaki.
 2. Nakiya.
 3. Algaragis.
 4. Dambun nama.
 5. Kilishi.
 6. Tsire.
 7. Daƙuwa. Kala biyu ce:
  • Daƙuwar aya.
  • Daƙuwar gyaɗa.
 8. Bakilawa.
 9. Alandaya.
 10. Dambun ƙwai.
 11. Wainar ƙwai.
 12. Maɗi.
 13. Alewa. Tana da nau’uka da yawa:
  • Farar alewa.
  • Alewar ɗinya.
  • Alewar gyaɗa da saurasu.

To ya zuwa wannan lokaci abin da ya samu kenan. Sannu a hankali idan ana ziyartar wannan shafi akai-akai za a riƙa cin karo da bayanai dalla-dalla game da kowane abinci da kuma yadda za a yi shi.

Abinci
Ɗakin Karatu

Harshen Turanci


Alƙur'ani


Jama'iyyun Siyasa

Kimiyyar Kwamfuta


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub