Adabin Turanci

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Adabin Turanci


Gabatarwa

Adabi, idan aka ce adabi a nan, kai tsaye ana nufin literature,  wanda kuma fanni ne na karatu a fagen karatun Turanci, wanda ya shafi dukkan  wasu abubuwa da ke gudana a rayuwar Turawa, saboda haka, al’amarin adabi, wani abu ne da ya shafi kowane mutum.

Adabin Turanci kamar kowane, yana da rassa guda biyu, adabin baka (Oral Literature), da rubutaccen adabi (literature). A wannan takarda, za mu fayyace haƙiƙanin menene shi adabin, amfaninsa, da kuma rabe-rabensa, da sauran su.

Ma’anar Adabi

Wannan kalma ta literature, tana da ma’anoni da dama. Za mu duba kaɗan daga ciki:

Literature tana da ma’ana ta rubutattun aikace-aikace kamar irin su rubutaccen ƙirƙirarren labari (fiction), waƙoƙi (poetry), wasan kwaikwayo (drama), da kuma suka (criticism), da ake ganin suna da muhimmanci a cikin harkar adabi (Encarta Dictionary, 2009; OALD, 2000). Sai kuma suka sake bashi wata ma’ana ta rubutaccen aikin da ya shafi al’ada, yare, jama’a, ko kuma wani ƙayadadden lokaci (Encarta Dictionary, 2009). Sannan kuma yana ɗaukar ma’ana ta dukkan wani rubutu da aka yi game da wani fanni (Ade, 2014; Jammaje, 2016; Britannica Ancylopeadia, 2010; Encarta Dictionary, 2009; OALD, 2000).

Idan kuma aka ce English Literature, to ana nufin rubuce-rubucen da aka yi a Ingila, tun daga zamanin tsohon Turanci (Old English) na ƙarni na 5, wanda yaren Jamusawa (German tribes), da magadansu da kuma tsofaffin mutanen Ingila waɗanda a dunƙulen ake kiran su da Anglo-Saxons a Turane suka gabatar (Microsoft Encarta, 2008).

Idan kuma aka ce Literature in English, to nan kuma ana nufin ayyukan Adabi (Literature) da aka yi cikin yaren Turanci a ƙasashen da Ingila ta rena kamar irin su Indiya, Ghana, Nijeriya, da sauran su (Jammaje 2016).

Amfanin Adabi

  1. Ilimantarwa: Adabi wata kafa ce ta samar da bayanan ilimi a wasu fannoni na rayuwa kamar irin su tarihi, siyasa da sauran su. Abubuwa kamar irin su waƙoƙi, da rubuce-rubucen marubuta, kan zama kafofin taskacewa, adanawa da kuma yaɗa bayanan ilimi.
  2. Nishaɗantarwa: Ayyukan adabi kan saka jama’a samun cikakken nishaɗi ta hanyar bayar da dariya, jin daɗi da kuma walwala.
  3. Koyar da Kyakkyawar Tarbiyya: Adabi, kyakkyawar kafa ce ta cusa kyawawan halaye a cikin zukatan yara. wannan kuma kan samu ta hanyar ƙirƙirarrun labaru, tatsuniyoyin mutanen Afirka, da sauran hanyoyi makamantansu.
  4. Wayar da kai: Wasu muhimman ayyukan adabi sukan zama kafa ta wayar da kan jama’a a nishaɗance kuma ta cikin hikima. Misali, waƙoƙi da kuma wasan kwaikwayo (drama).
  5. Wanzar da Al’adu da Tarihi: Adabi, wata babbar makaranta ce ta taskacewa tare kuma da yaɗa al’adun mutane da kuma tarihinsu. Ta wannan hanya ce tarihi da al’adu mutane ke wanzuwa iya tsawon zamani.

Rabe-Raben Adabi (Types of Literature)

Guda biyu ne kawai, sai kuma suka sake rarrabuwa kamar yadda za a gani a bigiren da ya dace:

  1. Adabin Baka (Oral Literature).
  2. Rubutaccen Adabi (Literature).

Manazarta:


Ade O. I. (2014). An Introduction to Literature and Literary Criticism. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: www.nou.edu.ng

Encyclopædia Britannica. (2010). Literature. Encyclopaedia Britannica Ultimate Reference Suite.  Chicago.

Jammaje K.M. (2016. English for Beginners and Literature for Beginners. Jammaje Academy, Kano-Nigeria.

Microsoft Student [DVD].  (2009). English Literature. Redmond, WA: Microsoft Corporation, 2008.

Oxford Advanced Learners Dictionary Six Edition (2000). Literature. Oxford University Press.

Harshen Turanci



Aikin Gona


Ɗakin Karatu


Alƙur'ani


Jama'iyyar PRP
Jama'iyyar NEPU
Jama'iyyar NPN


Abinci
Abinci...
Rabe-Rabe
Bitamin
Hanta


Kwamfuta
Amfanin Kwamfuta
Siffofin Kwamfuta
HTML
Algorizim
Ofareshin Risac


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub