Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar Dattawa - AmurkaTambarin Majalisar Dattawan Amurka   Hoto:U.S. Senate


Gabatarwa

Majalisar Dattawan Amurka, ita ce babbar Majalisa (Upper Chamber) wadda kuma ake kira Majalisar Dattawa (House of Senate). An kafa wannan Majalisa tun cikin shekarar 1789. Kenan, yau (2021), majalisar tana da shekaru 232 da kafuwa.

Majalisa ce mai wakilai 100 da ake zaɓo wakilai biyu daga kowace jahar Amurka guda 50 ba tare da fifiko ba ta hanyar la’akari da yawan jama’ar jaha kamar yadda yake a Majalisar Wakilai.

Tsayawa Zaɓe

Tanadi na farko, kashi na uku na Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya bayyana cewa: “Babu wani mutum da zai zama ɗan Majalisar Dattawan Amurka wanda bai kai shekaru talatin ba, kuma ba tare da zama ɗan ƙasar Amurka na tsawon shekaru tara ba, wanda kuma bai zamo mazaunin jahar da za a zaɓe shi ba”. Kenan, sai ya cika waɗannan sharuɗa:

  1. Zamowa ɗan shekaru talatin zuwa sama. Damar da shugaban Amurka mai ci (2021), Joseph Robinette Biden Jr. ya samu aka zaɓe shi yana ɗan shekaru 39 abin da ya bashi damar zama ɗan Majalisar Dattawa mafi ƙarancin shekaru a Karon farko.
  2. Ɗan Ƙasar Amurka wanda ya shekara tara cur da zama ɗan ƙasa.
  3. Mazaunin jahar da zai wakilta idan aka zaɓe shi.


Tambarin Majalisar Dattawan Amurka   Hoto:U.S. Senate

Zaɓe

Da farko, kuma a tanadin Kundin Tsarin Mulkin Amurka na farko, na 1789, naɗa ɗan Majalisar Dattawa ake yi. Wadda kuma jahohi ne ke naɗa wanda suke son ya wakilce su a wannan majalisa ta Dattawan Amurka.

Amma daga baya, biyo bayan gyaran fuskar karo na 17 da aka yi wa Kundin Tsarin Mulkin a cikin shekarar 1913, sai rawa ta canja sakamakon canjin kiɗa, wadda ya sauya akalar lamarin zuwa zaɓe.

Wa’adin Mulki

Ana zaɓar dukan Ɗan Majalisar Dattawan Amurka ne domin ya yi wa’adin shekaru 6 cur, duk da cewa, akwai wata ‘yar sarƙaƙiya ta sake zaɓen ɗan Majalisar Dattawan duk bayan shekaru biyu.

Shugabanci

Mataimakin shugaban ƙasar Amurka, shi yake zama shugaban Majalisar Dattawan Amurka, tare da samun ‘yancin kaɗa ƙuri’a a lokacin raba gardama. Abin nufi, idan wata gaɓa ta zo da aka kaɗa ƙuri’a domin wani lamari, sai adadin ya yi kan-kan-kan, to a nan sai shi ma mataimakin shugaban ƙasa ya kaɗa tasa ƙuri’ar domin a samu ɓangaren da zai yi rinjaye. Amma idan ba haka ba, to fa shi ɗan sasanto ne.

Iko

Abin da ake nufi da iko a nan shi ne ƙarfin faɗa-a-ji na wannan zaure na sanatoci. Wadda kuma, bisa sahalewar Kundin Tsarin Mulkin Amurka, su suke da damar tantance naɗe-naɗen shugaban ƙasa a gurin da ake da buƙatar haka da kuma tabbatar da yarjeniyoyi. Ƙari a kan wannan kuma su ne suke da damar tabbatar da tsige wasu jami’an gwamnatin tarayya idan Majalisar Wakilai ta turo musu.

Manazarta

Library of Congress (Babu Shekara). About the Congress. An ciro a 2021, daga https://www.congress.gov/about

The White House (Babu Shekara). The Legislative Branch. An ciro a 2021, daga https://obamawhitehouse.archives.gov/1600/legislative-branch

United States Senate (2019). Class I - Senators Whose Term of Services Expire in 2025. An ciro a 2021, daga https://www.senate.gov/


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub