Me ka ke nema?


Shafin Farko

Babajide Olusola Sanwo-OluGwanmnan Lagos Babajide Olusola Sanwo-Olu

Gabatarwa

Babajide Sanwo_Olu, shi ne zaɓaɓɓen gwamnan Jahar Lagos a Jamhuriyar Tarayyar Najeriya. Ɗan kasuwa; ma’aikacin banki daga baya kuma ɗan siyasa da ya fara siyasa a shekarar 2003 a matakin mai bai wa mataimakin gwamnan Lagos na lokacin shawara har zuwa ɗarewar sa kujera mafi daraja a Jahar Lagos. An haife shi a shekarar 1965. Ya yi karatu har zuwa matakin digiri na biyu da kuma ƙarin samun horo a wasu fannonin ilimi a nan gida da kuma ƙasashen waje. Magidanci ne shi mai mata ɗaya da ‘ya’ya huɗu.

Haihuwa

Babajide Olusola Sanwo-Olu, haifaffen garin Lagos ne da aka haifa a ranar 25 ga watan  Juli na shekarar 1965; kenan ya zuwa wannan lokaci yana da shekaru 55 (1965 – 2020) da haihuwa. Ɗa ne shi ga fitacciyar zuriyar Sanwo-Olu da ke Tsibirin Lagos (Lagos Island).   

Karatu

Babajide Olusola ya yi karatunsa na firmare a Makarantar Gwamnati da ke Surulere, Lagos (Government Demonstration School, Surulere, Lagos) daga nan kuma ya samu zuwa Makarantar Sikandire ta Ijebu-Ife a jahar Ogun (Ijebu-Ife Grammar School, Ogun State).

Ya samu nasarar shiga Jami’ar Lagos (University of Lagos) inda ya samu digirin farko a fannin Surveying & Geo-Informatics da kuma digiri na biyu Master of Business Administration (MBA) duk a jami’ar.

Haka nan kuma ya samu halartar wasu kwasa-kwasai a fannin kasuwanci daga fitattun manyan makarantu a duniya da suka haɗa da  Harvard Kennedy School of Government; London Business School da kuma Lagos Business School.

Gogayyar Aiki

Babajide Olusola Sanwa-Olu, gogaggen ma’aikacin banki ne sannan kuma fitaccen ɗan siyasa. Yana da ƙwarewa a harkar banki ta tsawon shekaru uku (1994 -1997).

Ya yi aiki a bankunan Lead Merchant Bank a matsayin ma’ajiyi (Treasurer); United Bank for Africa (UBA), a matsayin shugaban sashen hada-hadar kuɗaɗen waje (Head of Foreign Money Market); First Inland Bank Plc, wanda yanzu ya koma First City Monument Bank, a matsayin mataimakin babban manaja, sannan kuma shugaban sashe (Deputy General Manager and Divisional Head). Daga wannan banki kuma sai ya yi murabus daga aikin bankin sannan ya tsunduma harkokin kasuwanci.

Siyasa

Shekarar 2003, ita ce tubalin ginin siyasar Babajide Olusola Sanwo-Olu inda aka naɗa shi a matsayin mashawarci na musamman (Special Adviser) ga mataimakin gwamnan jahar Lagos, Femi Pedro a fannin Corporate Matters. Daga baya a cikin shekarar 2004, aka ɗaukaka matsayin nasa zuwa mashawarci na musamman ga gwamnan Lagos, Bola Ahmed Tinubu duka dai a fanni guda.

An yi masa muƙamin kwamishinan wucin-gadi na ma’aikatar tsara tattalin arziƙi da kasafin kuɗi (Acting Commissioner for Economic Planning & Budget) daga shekarar 2004 zuwa 2005; kwamishinan ma’aikatar cinikayya da masana’antu (Commissioner for Commerce and Industry) a shekarar 2007; kwamishinan ma’aikatar Ministry of Establishments, Training and Pensions duka a shekarar 2007.

A shekarar 2016, gwamnan Lagos, Akinwunmi Ambode ya yi masa naɗin babban jami’i (Managing Director/CEO) a ma’aikatar Lagos State Development and Property Corporation (LSDPC), kujerar da ya ci gaba da zama a kanta har zuwa lokacin tsayawarsa takarar neman kujerar gwamna.

Ƙungiyoyin Ƙwararru

Babajide Olusola Sanwo-Olu, mamba ne a wasu ƙungiyoyin ƙwararru. Daga ciki akwai

 • Mamba a Chartered Institute of Personnel Management (CIPM.
 • Mamba a Institute of Directors (IOD).
 • Mamba a Chartered Institute of Personnel Management (CIPM).
 • Mamba a Nigeria Institute of Training and Development (NITAD).

Lambobin Yabo da Girmamawa

Zamowar Babajide Olusola Sanwo-Olu mutum mai son hidimtawa jama’arsa, ta saka shi samun lambobin yabo da kyaututtukan girmamawa masu tarin yawa. Ga wasu kaɗan da muka kalato daga Wikipedia (2019) da kuma Good Read (2019):

 • Platinum award from the Lagos State Public Service Club.
 • 2009 Best in Human Capital Development award from the Industrial Training Fund (ITF).
 • Merit award from the Association of National Accountants of Nigeria.
 • National Association of Nigerian Nurses and Midwives Gold Mentor Appreciation Award.
 • Merit award from the Chartered Institute of Personnel Management in Nigeria (CIPMN).
 • Merit Award from the Association of Professional Women Engineers of Nigeria (APWEN).
 • Nigerian Union of Teachers Excellence Award for Contribution to Upliftment of Education.
 • LSDPC Impactful Leadership and Recognition Award.
 • Young Christian Fellowship Appreciation Award.
 •  University of Lagos International School Parents-Teachers Association Recognition & Appreciation Award.
 •  University of Lagos Alumni Association Merit Award for Outstanding Commitment and Contributions to National Development.

Gwamna

A ranar 16 ga watan Satumban shekarar 2018, Babajide Olusola Sanwo-Olu ya yanki tikitin nuna sha’awar neman jama’iyyarsa ta APC ta sahale masa ta tsayar da shi takarar Gwamnan Jahar Lagos. Buƙata da ta samu karɓuwa bayan lashe zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a cikin gidan jama’iyyar reshen jahar Lagos a ranar 2 ga watan Oktoban 2018. Nasarar tasa ta biyo bayan gagarumin goyon baya da ya samu daga masu ruwa-da-tsaki a cikin jama’iyyar.

Ya samu nasarar zama Gwamnan Jahar Lagos bayan gagarumar nasarar da ya samu da yawan ƙuri’un da suka kai 739,445 a babban zaɓen da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2019.


Babajide Olusola Sanwo-Olu yana karɓar takardar shedar cin zaɓe
Hoto: The Source

Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta (INEC), ta ayyana zamowar Babajide Olusola Sanwo-Olu gwamnan Lagos a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2019. Ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin Gwamnan Jahar Lagos na 15 a ranar Laraba 29 ga watan Mayun shekarar 2019 a babban filin taro na Tafawa Ɓalewa da ke Tsibirin Lagos (Lagos Island).


Babajide Olusola Sanwo-Olu yana rantsuwar kama aiki
Hoto: Pulse

Iyali

Babajide Olusola Sanwo-Olu yana da mata guda ɗaya; Likita Dr Mrs Ibijoke Sanwo-Olu. Suna da ‘ya’ya guda huɗu.

Manazarta:

Sanwo-Olu B. (2019). Where It All Began. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://www.babajidesanwoolu.com/pages/about

Egbas J. (2019). Read what Sanwo-Olu said when he was sworn in as Lagos Goɓernor. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.pulse.ng/news/politics/read-what-sanwo-olu-said-when-he-was-sworn-in-as-lagos-governor/gm8t8gr

Good Read Biography (2019). Babajide Olusola Sanwo-Olu Biography. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://www.goodreadbiography.com/babajide-olusola-sanwo-olu-biography/

Lagos State (2019). Babajide Sanwoolu, Governor of Lagos. An ciro a shekarar 209 daga shafin: https://governor.lagosstate.gov.ng/babajide-sanwoolu-goɓernor-of-lagos-state/

LASEPA (2014). THE Management Team; Babajide Sanwo-Olu. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: http://lasepa.gov.ng/sanwo.htm

Nollywood (2019). Babajide Sanwo Olu Biography [and Wife]. An ciro a shekarar 2019 daga shafin:https://nolly.com.ng/babajide-sanwo-olu-biography/

Wikipedia (2019). Babajide Sanwo-Olu. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Babajide_Sanwo-Olu

 


Tarihin Najeriya
Tarihin Jahar Lagos

Gwamnoni

 • Babajide Sanwo Olu
 • Mr Akinwunmi Ambode – 2015 – 2019
 • Mr. Babatunde Raji Fashola, SAN 2007-2015
 • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu 1999-2007
 • Brig-Gen. Mohammed Buba Marwa 1996=1999
 • Col. Olagunsoye Oyinlola 1993-1996
 • Sir Michael Agbolade Otedola 1992- 1993
 • Brig-Gen. Raji Alagbe Rasaki 1988-1991
 • Navy Captain Mike Okhai Akhigbe 1986-1988
 • Air Cmdr. Gbolahan Mudashiru 1984-1986
 • Alhaji Lateef Kayode Jakande 1979-1983
 • Navy Cmdr. Ebitu Ukiwe 1978-1979
 • Navy Cmdr. Ndubuisi Kanu 1977-1978
 • Navy Cmdr. Adekunle Lawal 1975-1977
 • Brig-Gen. Mobolaji Johnson 1967-1975

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub