Beta Sel

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bela SelHoto: Diabetes UK


Gabatarwa

Beta sel, wanda kuma ake kira beta cell a Turance, sannan ake rubuta shi da β-cell a taƙaice, wata ƙwayar halitta ce ta musamman a cikin fankiris wadda ke samarwa, adanawa da kuma sakin sinadarin insulin. Tana daga cikin ƙwayoyin halitta biyar da ake kira Islet waɗanda ke da alhakin samarwa tare kuma da harba sinadaran hormones kai tsaye zuwa cikin magudanar jini (bloodstream).

Aiki

Babbar gudunmawar da wannan ƙwayar halitta ke bai wa gangar jiki ita ce samarwa tare kuma da harba sinadarin insulin wanda ke da alhakin daidaita sinadarin bilkodin cikin jini.

Gazawa

Gazawar aikin wannan ƙwayar halitta yana bambamta da nau'in ciwon sukari.

  1. Ciwon sukari nau'in farko: A nan, beta sel yana mutuwa ne murus, sakamakon hare-hare da garkuwan jiki ke kawo masa bisa ruɗani. Biyowa bayan wannan mutuwa tasa kuma sai sashen jiki na fankiris ya daina samar da sinadarin insulin kwata-kwata, shikenan, cutar sukari nau'in farko ta samu.
  2. Ciwon sikari nau'i na biyu: A wannan yanayin kuma, jiki yana bijirewa sinadarin insulin ne tare da yunƙurin samar da insulin mafi inganci.

Waɗannan su ne gurare biyu da beta sel ke da rawar takawa a harkar ciwon sukari. Allah Ka ƙara kiyaye mu.

Manazarta:


Manazarta
Cantley J. da Ashcroft F.M. (2015). Q&A: insulin secretion and type 2 diabetes: why do β-cells fail? An ciro a 2021, daga https://bmcbiol.biomedcentral.com/articles/10.1186/s12915-015-0140-6
 
Cerf M.E. (2013). Beta Cell Dysfunction and Insulin Resistance. An ciro a 2021, daga https://www.ncbi.nlm.nih.gov/pmc/articles/PMC3608918/

Diabetes Digital Media Ltd (2019). Beta Cells. An ciro a 2021, daga https://www.diabetes.co.uk/body/beta-cells.html

Science Direct (2017). The dynamic plasticity of insulin production in β-cells. An ciro a 2021, daga https://www.sciencedirect.com/science/article/pii/S2212877817301795


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub