Ciwon Sukari Yayin Goyon Ciki

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ciwon Sukari Yayin Goyon Ciki'Ya'yan Fenugirik (Fenugreek Seed). Amfani da su yana warkar da ciwon sukari
Hoto: Encyclopaedia Britannica


Gabatarwa

Shi ciwon sukari yayin goyon ciki, ciwon sukari ne da kawai mata masu juna biyu yake kamawa. Sauyin yanayi da jiki ke samu a yayin goyon ciki, shi ne babban abin da ke haifar da wannan ciwo, kuma wani abin daɗi shi ne sau da yawa da zarar an rabu da cikin shikenan cutar ta tafi. Healthline (2018), suka ce: “Ciwon yana shafar mata ne a zamanin goyon ciki”. Wannan ciwo shi ake kira Gestational diabetes a Turance. Javanov (2017) ya ce: “Ciwon sukari yayin goyon ciki shi ne yawaitar sinadarin sikarin jini a yayin goyon ciki”.

Sababi

Sauyin yanayin sinadarin da ke da ruwa da tsaki wajen tunkuɗa sinadarin insulin cikin jini a zamanin goyon ciki, shi ke haddasa wannan cuta. Javanov (2017), ya ce: “Ƙwayoyin halittar da ke toshe sinadarin insulin da mahaifa (placenta) ke samarwa su ke haifar da wannan ciwo”.

Haka nan ma kuma dai, mata masu nauyin da ya wuce misali ko kuma nauyinsu yake ƙaruwa a yayin goyon ciki, suna fuskantar barazanar kamuwa da wannan cuta.

Alamomi

Healthline (2018), suna bayyana cewa, “Mafiya yawan matan da ke kamuwa da wannan cuta basa nuna wata alama. Sai dai, ana gane wannan yanayi ne a yayin awo ko gwajin sikari kamar yadda aka saba yi a tsakanin sati na 24 zuwa na 28 da samuwar ciki”. Amma duk da haka, a kuma yanayin da ba kasafai ba, akan samu ƙaruwar yin fitsari da kuma ƙishin ruwa a matsayin alamar kamuwa da wannan cuta.

Hatsari

Mata masu juna biyu da:

  1. Shekarunsu suka haura 25.
  2. Mata masu nauyi maras misali.
  3. Matar da ta taɓa kamuwa da wannan cuta a baya.
  4. Matar da ta taɓa haifar jaririn da nauyinsa ya haura fan 9 (9 pounds).
  5. Matar da zuriyarsu suke da tarihin ciwon sukari nau’i na biyu.

Suna daga cikin jerin matan da suke fuskantar barazanar kamuwa da wannan cuta a lokacin goyon ciki.

Magani

Motsa jiki da kuma samun ingantacen abinci, su ne muhimmai. Idan kuma lamari ya ta’azzara, to a hanzarta ganin likita.

Manazarta:


Cleveland Clinic (2018). Diabetes: An Overview. An ciro a 2021, daga https://my.clevelandclinic.org/health/diseases/7104-diabetes-mellitus-an-overview

Healthline (2018). Everything You Need to Know About Diabetes. An ciro a 2021, daga https://www.healthline.com/health/diabetes

Jovanov D. (2017). Herbs and Spices for Diabetes. International Journal of Nutritional Science & Food Technology. 3:1, 26-29. DOI: 10.25141/2471-7371-2017-1.0026


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub