Ciwon Sukari

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ciwon SukariHoto: WHO International


Gabatarwa

Ciwon sukari, abin da ake kira diabetes a Turance, cuta ce mai matuƙar hatsarin gaske wadda ƙarancin sinadarin insulin a jiki ko gajiyawar sassan jiki wajen aiki da shi ke haifarwa.

Gammayar Masu Ciwon Sukari ta Duniya; wato International DiabetesFederation, ta ayyana cewa akwai mutane kusan miliyan ɗari biyar (500 Millions) da ke ɗauke da wannan cuta a faɗin duniya, International Diabetes Federation (2021). Tare da cewa wannan cuta ita ce ta bakwai wajen yawan kashe mutane a duniya kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana, WHO (2021).

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana wannan cuta a matsayin mai haddasa makanta, gazawar ƙoda (kidney failure), bugun zuciya (heart attack), shanyewar ɓarin jiki (stroke) da kuma cire ƙafa; daga guiwa zuwa ƙasa abin da a Turance ake kira lower limb amputation, WHO (2021).

Sai dai, duk da haka, Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta tabbata da cewa cin lafiyayye abinci mai gina jiki (Healthy diet), motsa jiki, da kuma rashin shan taba za su iya kare mutum daga kamuwa da ciwon sukari nau’i na biyu (type 2 diabetes).

Duk da wannan barazana da wannan mugun ciwo na sukari ke yi wa rayuwar ɗan’adam, to ɗan’adam ɗin ya zurfafa bincike ta yadda ya gano hanyoyin da idan aka bi su a kimiyyance za a kaucewa kamuwa da wannan cuta waɗanda suke da ita kuma za su waraka.

Bisa waɗannan dalilai ne ma ya saka Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware Ranar 14 ga watan Disambar kowace shekara a matsayin Ranar Ciwon Sukari ta Duniya.

Rumbun Ilimi, ya ƙuduri aniyar yin warwara game da wannan cuta bisa dogaro da binciken da ƙwararru a fannin lafiya suka gudanar. Muna roƙon Allah Ya baiwa dukkan masu ɗauke da wannan cuta lafiya, waɗanda kuma basu kamu ba Allah Ya daɗa kare su. A yi karatu lafiya.

Ciwon Sukari

Ciwon sukari kai tsaye shi ne yawaitar sinadarin bilkodi (high levels of blood glucose); wato sukari (blood sugar) a cikin jini (bloodstream). Wadda kuma za a ce, cuta ce da ta shafi gazawar sassan jiki wajen daidaita sinadarin bilkodi (glucose) a cikin jini wadda kan faru sakamakon rashi, ƙaranci ko gazawar sassan jiki wajen yin aikin da ya dace da sinadarin insulin, wadda daga ƙarshe yake kaiwa ga lalata zuciya, magudanar jini, jijiyoyi, ƙoda da kuma idanuwa. Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO, (2021): Dakta Taylor, (2019); da kuma Britannica (2021).


Hoto: WHO International

A duk lokacin da mutum ya ci abinci, wasu sinadaran enzayims (enzymes) za su markaɗa wannan abinci su cire sinadarin kabohaidiret tare kuma da mayar da shi zuwa bilkodi, wanda wannan bilkodi shi ne sukari kuma shi ne sinadarin da yake bai wa dukkan jiki kuzari (energy).

Abin da zai biyo bayan wannan shi ne shigar wannan bilkodi cikin jini abin da daga ƙarshe zai zama sukarin jini (blood sugar) wanda kuma sinadarin insulin zai biyo bayansa domin ya daidata shi ta hanyar taimakawa duk wata tsoka da ke cikin jikin ɗan’adam ta tsotsi adadin da take da buƙata na wannan sukari domin da shi take samun kuzari. Abin da ya yi rara kuma sai a a tura shi zuwa ma’adana. Idan har haka tana wakana, babu makawa jiki zai zauna lafiya tare kuma da yin aikin da ya dace da shi.

Idan aka samu akasi, sinadarin insulin ya yi ƙaranci, ko kuma sassan jiki da ke cuɗanya da shi suka gaza yin aiki tare da shi kamar yadda ya dace, to bilkodi zai yi ta taruwa a cikin jini, abin da daga ƙarshe zai haifar da yawaitarsa a cikin jini. Wannan yawa da bilkodi ya yi a cikin jini shi ne cutar sukari wadda ke haddasa dukkan bala’o’in da ke tare da ciwon sukari.

Nau’ukan Ciwon Sukari

Masana sun kasa ciwon sukari hawa uku:

  1. Gajeren ciwon sukari (Prediabetes).
  2. Ciwon sukari nau’in farko (Type 1 Diabetes).
  3. Ciwon sukari Nau’i na biyu (Type 2 Diabetes).
  4. Ciwon sukari a lokacin goyon ciki (Gestational diabetes).

Hatsari

Ciwon sukari cuta ce mai tsananin hatsari, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ayyana ta a matsayin cuta ta bakwai a cikin jerin cututtukan da suka fi kashe mutane a duniya.

Duk cikin sakankuna 5 mutum guda yana kamuwa da ciwon sukari, duk cikin sakankuna goma, mutum guda yana mutuwa sakamakon ciwon sukari, haka nan kuma duk cikin sakankuna talatin, ana cire ƙafa guda sakamakon ciwon sukari.

Illoli

Manya-manyan illolin ciwon sukari sun haɗa da haifar da cututtukan da suka haɗa da: makanta, gazawar aikin hanta, ciwon zuciya, shanyewar ɓarin jiki, da kuma haddasa cire ƙafa da sauransu.

Manazarta:


Bratannica (2021). Diabetes mellitus medical disorder. An Ciro a shearer 2021 data shafin: https://www.britannica.com/science/diabetes-mellitus

Dansinger M. (2019). Prediabetes (Borderline Diabetes). An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.webmd.com/diabetes/what-is-prediabetes

United Nations (2021). World Diabetes Day 14 November. An ciro a shearer 2021 data shafin: https://www.un.org/en/observances/diabetes-day

WHO (2021). Diabetes. An ciro a shearer 2021 data shafin: https://www.who.int/health-topics/diabetes#tab=tab_1

WHO (2019). Classification of Diabetes Mellitus.  World Health Organization.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub