Shafin Farko

Dabbobi


Gabatarwa

Kafofin da ke bayyana tarihi da suka haɗa da sassaƙe-sassaƙe, zane-zane, da sauransu da aka adana sama da shekaru dubu arba’in da suka shuɗe (40,000) sun nuna akwai dangantaka ta kusa-da-kusa kuma mai tarin fa’idodi tsakanin dabbobi da mutane.

Duk da bambance-bambancen da ke akwai ta fuskar amfani da dabbobi a faɗin duniya, an samu cewa mutum yana amfani da dabbobi a matsayin abinci, sutura, kafar samun ilimi, makamashi, hanyar sufuri, ƙawance, nishaɗantarwa, kafar samun kuɗin shiga, da sauransu. Haka nan kuma suma dabbobi sun dogara da mutum wajen samun abinci, kariya, muhalli da ƙawance.

Zamantakewar muhalli ita ta ƙulla wannan dangantaka tsakanin dabbobi da mutane. Kamar yadda zai zo nan gaba.


Kaza ɗaya daga cikin abubuwan gida

Amfanin Dabbobi

  • Fannin Likitanci da Harhaɗa Magunguna
  • A wannan fanni ana amfani da dabbobi wajen gwaje-gwajen magunguna kasancewar akwai kamanceceniyar ƙwayoyin halitta da ke akwai tsakanin dabbobi da mutane. Ana amfani da su wajen:

    1. Gwada maganin rigakafin cutar shan'inna, baƙon dauro, d.s.
    2. Gwada maganin kashe ƙwayoyin cutar bakteriya (bacteria).
    3. Gwada ƙwayar maganin cututtukan da suka shafi ciwon suga, hawan jini, da dangoginsu.
    4. Jarraba fiɗar cire cutar zuciya.
    5. Jarraba dashen sassan jiki kamar dashen ƙoda da sauransu.
    6. Gwada maganin cutar hauka.
    7. Gwada warkar da cutar bugun zuciya da shanyewar tsagin jiki.
    8. Gwada maganin cire dattin giya da sauran kayan maye.
    9. Jarraba warkar da cutar huhu.
    10. Jarraba warkar da cutar daji.
  • Aikin Gona
  • Amfanin dabbobi a wannan fanni wani abu ne da ke a bayyane ƙururu. A wannan zamani da muke ciki amfanin dabbobi a aikin gona abu ne mai wahalar iyakancewa, amma daga ciki akwai:

    1. Samar da abinci: Su dabbobin a kan-kansu ana kiwata su a matsayin noma. Wanda kuma wannan ke da ɗimbin amfani da ya haɗa da samar da abinci kamar irin su nama da madara.
    2. Maganin zaizayar ƙasa: Ana amfani da kashin dabbobi da kuma turɓayar abincin da dabbobi suka ci musamman ciyawa wajen magance zaizayar ƙasa.
    3. Samar da taki: Ana amfani da kashin dabbobi musamman shanu, awaki, tumaki da makamantansu wajen yin taki.


    Ana Huɗa da shanu a gona

  • Harkar Sufuri

  • Jaki ɗauke da kaya

    Ana amfani da dabbobi kamar irin su raƙumi, doki, da jaki wajen sufuri. Bincike ya tabbatar da cewa idan aka kimanta darajar sufurin dabbobi da kuɗi a ƙasar Indiya, zai iya kaiwa ƙimar Dalar Amurka Billiyan Biyar. Idan kuma aka ce za a musanya shi da hanyar sufuri ta zamani (wato kamar a dakatar da amfani da dabbobi a cikin harkar sufuri a iya faɗin ƙasar), to ana buƙatar kuɗi kimanin Dallar Amurka Biliyan Shida domin sayo ababen sufurin da za su maye gurbin dabbobin. Sannan kuma an yi ƙiyasin cewa harkar sufurin Jakuna a Saharar-Afirka ta kai jaki dubu a cikin shekarar 1960s wanda ya zuwa yanzu kuma ta haɓɓaka har zuwa dubu saba'in da biyar (wato yawan jakunan da ake amfani da su a shekarar 2009 a harkar sufuri a yankin Saharar-Afirka sun kai dubu saba'in da biyar bisa ƙiyasi). Kendall (2009).


    Raƙumi ɗauke da kaya

  • Tattalin Arziƙi
    Binciken masana ya tabbatar da cewa dabbobi kyakkyawar kafa ce ta haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasahe. A cikin binkensa (Ladislav, 2012), ya bayyana cewa a cikin shekarar 2007 ƙasashen Turai guda 28 da ke cikin Tarayyar Turai (EU) sun samar da Yuro Biliyan 335 a fannin gona wanda kaso 42.7 na yawan kuɗaɗen da suka samar a cikin gida wanda kuma Yuro biliyan 143.045 na kuɗin ya fito ne daga fannin dabbobi.

    Har-wa-yau dai, (Kendall, 2009), sun tabbatar da cewa binciken masana ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar nan gaba a riƙa amfani da tataccen kitsen 'yantsaki a madadin man fetur wanda wannan ka iya rage yawan dogaro da kuma maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa a fannin man fetur.

Manazarta:


Godfrey A. S. (2015). The Importance of Veterinary Medicine to Livestock Health. An ciro daga https://www.bahamas.gov.bs/

Kendal (2009). The Importance of Animals. An ciro daga https://www.toxicology. org/pubs/docs/air/AIR_Final.pdf

M. (2012). Economics and animal health: the importance of animal health and the EU added value. Food Chain Directorate-General for Health and Consumers European Commission, Brussels. An ciro daga ec.europa.eu/dgs/.../03102012_presentations_1_ladislav_miko_en.pdf

William H. M. (2010). Saving Human Lives: The Importance of Animal Research in Biomedical Science. An ciro daga www.fecava.org/.../The%20 economic%20importance%20of%20Compan

Aikin Gona



Ɗakin Karatu

Harshen Turanci


Alƙur'ani


Jama'iyyar PRP
Jama'iyyar NEPU
Jama'iyyar NPN


Abinci
Abinci...
Rabe-Rabe
Bitamin
Hanta


Kwamfuta
Amfanin Kwamfuta
Siffofin Kwamfuta
HTML
Algorizim
Ofareshin Risac


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin