Sarakunan Dutse

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarakunan Dutse


Gabatarwa

Masarautar Dutse na daga cikin masarautu masu daɗaɗɗen tarihi. Sai dai, ta samu tasgaro a wasu lokuta a baya, musamman zamanin da sarkin Kano Abdullahi Barja ya yaƙeta ta koma ƙarƙashinsa. Saboda waɗannan dalilai da ma wasu, sai ya zamo wasu sarakunan na Dutse a wasu lokuta a baya suna a matsayin hakimai ne ƙarƙashin masarautar Kano.

Wannan masarauta ta Dutse, tana da gidajen sarauta guda uku kamar haka: Barebari (Kanuri), Haɓe (Hausawa), da kuma Fulani (Fulata-Barno).

Daga wancan lokaci zuwa yau (2016), wannan masarauta ta samu sarakuna 47. Na farkonsu shi ne Sarki Tuwai Mai Asarki Babba, na ƙarshe kuma ya zuwa yanzu (2016), shi ne mai martaba sarki sarki Nuhu Muhammadu Sanusi, CFR. Kamar yadda za a ga jerin sunayensu a ƙasa:

Sarakunan Haɓe (Hausawa)

  1. Sarki Tuwai Mai Asarki Babba 1421 – 1463
  2. Sarki Ƙetare Ɗan’auta Mai Kuka 1463 - 1463
  3. Sarki Tasau Ɗan Ƙetare 1463 – 1476
  4. Sarki Maido Mai Asarki Ƙarama 1476 – 1482
  5. Sarki Maigiji-Tandu 1482 - 1489
  6. Sarki Amdu Maranje 1489 – 1498
  7. Sarki Babilu Mai Karauna 1498 – 1515
  8. Sarki Labun Mai Achiza 1515 – 1528
  9. Sarki Yakwabu Kwasau 1528 – 1554
  10. Sarki Sambore Mai Jugurgur 1554 – 1564
  11. Sarki Dunhu Ɗan Maryama 1564 - 1569
  12. Sarki Akuli Gurumfa 1569 – 1577
  13. Sarki Mantau Jarmai Babba 1577 – 1584
  14. Sarki Jawandu-Dogo 1584 – 1609
  15. Sarki Yusufu Atakalafiya 1609 – 1616
  16. Sarki Mamman Tauroma Mai Babban Wando 1616 – 1632
  17. Sarki Yakubu Nabukka 1632 – 1643
  18. Sarki Inuwa Bagizire 1643 – 1658
  19. Sarki Habu Mai Ƙoƙiya 1658 – 1667
  20. Sarki Audu Idon Mikiya 1667 – 1679
  21. Sarki Mani Mai Artabu 1679 – 1686
  22. Sarki Hassan Makau Dodon Bango 1686 – 1702
  23. Sarki Mamman Mai Sajen Fama 1702 – 1720
  24. Sarki Yahai Maƙuri Bangon Dutse 1720 – 1732
  25. Sarki Ada Gyauron Maza 1732 – 1735
  26. Sarki Zubairu Tsohon Mutum 1737 – 1797
  27. Sarki Mamman Natata 1797 – 1799
  28. Sarki Amadu Gwajabo 1799 – 1807

Sarakunan Fulani

Dangane da sarautar Fulani a Masarautar Dutse akwai gidaje guda biyu da suka sarautar Dutse tun daga shekarar 1807 bayan samun nasarar jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo zuwa yau. Akwai ƙabilar Jalligawa da kuma Yalligawa.

  1. Sarki Salihu Ɗan Ibrahim 1807 – 1819.
  2. Sarki Musa Ahmadu 1819 – 1840.
  3. Sarki Bello Ɗan Musa 1840 – 1849
  4. Sarki Suleman Ɗan Musa 1849 – 1868.
  5. Sarki Ibrahim Ɗan Salihu 1868 – 1884.
  6. Sarki Abdulƙadir Ɗan Salihu 1884 – 1893
  7. Sarki Salihu Ɗan Ibrahim II 1893 – 1894
  8. Sarki Ibrahim Ɗan Musa 1894
  9. Sarki Abdulƙadir Ɗan Musa 1894 – 1901
  10. Sarki Abduƙadir Ɗan Ibrahim 1901 – 1903
  11. Hakimi Haladu Ɗan Suleman 1903 – 1910
  12. Hakimi Halilu Ɗan Bello 1910 – 1911
  13. Hakimi Hamidan Ɗan Ibrahim 1912
  14. Hakimi Abdullahi Ɗan Suleman 1912 – 1919
  15. Hakimi Bello Ɗan Abdulƙadir 1919 – 1923
  16. Hakimi Suleman Ɗan Nuhu 1923 – 1960
  17. Sarki Abdullahi Maikano Ɗan Sulemanu `1960 – 1983
  18. Sarki Muhammadu Sanusi Ɗan Bello 1983 – 1995
  19. Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi 1995 zuwa yau

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub