Hakimin Dutse Abdullahi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abdullahi Ɗan Suleman 1912 – 1919 (Hakimi)


Gabatarwa

Abdullahi Ɗan Suleman Bayallige, shi ne hakimin Dutse na Huɗu. Sarkin Kano Muhammadu Abbas (1903 – 1919), shi ya naɗa shi a kan wannan kujera bayan rasuwar Haminda Ɗan Ibrahim (1912). Yanzu sarauta ta sake komawa gidan Yalligawa kenan.

Abdullahi Ɗan Suleman ya hau wannan kujera da ƙafar dama, inda ya yi ƙoƙari ya haɓɓaka yawan kuɗaɗen harajin da yake karɓa dan gujewa abubuwan da suka wakana a baya. Sai dai kash! Masu iya magana sun ce, da muguwar rawa gwamma ƙin tashi. Wannan ƙara yawan kuɗin haraji da sabon hakimi ya yi, ya ƙara yawaitar masu ƙaura daga Ƙasar ta Dutse zuwa ƙasashen Birnin-Kudu da Gaya waɗanda su yawan nasu harajin bai kai na Dutsen ba. A saboda haka abin da ake gudun faruwarsa sai ya faru. Abin ya kasa kasau, kuɗaɗen da ake tattarawa na haraji suka yi baya sosai musamman a cikin shekarar 1914/1915. Saboda haka a shekarar 1916 sai Turawa suka zarge shi da gazawa wajen gudanar da aiki, sannan kuma suka umarci Sarkin Kano Muhammadu Abbas (1903 – 1919) da ya rage darajar Sarki Abdullahi ta hanyar naɗa Ɗan-Lawan Ahmadu Gurara a matsayin mataimakinsa.

Bisa dagewa da shi Ɗan-Lawan ya yi wajen tattara kuɗaɗen harajin, sai kuɗaɗen shekarar 1916/1917 ya fi na baya. Ganin haka sai ta saka Turawa samun ƙwarin guiwar tabbatar da Ɗan-Lawan Ahmadu Gurara a matsayin Hakimin Dutse. Daboda haka sai suka umarci Hukumar Gargajiya (Native Autothrity) da ta rage darajar Sarki Abdullahi zuwa dagaci, shi kuma Ɗan-Lawan a ɗaukaka shi zuwa hakimi.

Wannan abu da ya faru ya saɓa yarjejeniyar da ke tsakanin masarautar Dutse da kuma ta Kano tun farkon samun nasarar jihadi a shekarar 1803, saboda haka sai gidajen sarautar Dutse (Jalligawa da Yalligawa) suka haɗe kansu, suka yi bore, sannan suka daina amincewa da duk wani naɗi da za a yi, sannan suka ƙi baiwa Ɗan-Lawan haɗin kai. Wannan kuma ta hana shi Ɗan-Lawan ɗin aikata kataɓis a Dutse. Lamari ya cakuɗe ta yadda Fadar Masarautar da ke Garu ta gagari Ɗan-Lawan shiga sai dai ya fara aiwatar da ɗan abin da ba a rasa na mulki daga gidansa da ke Limawa.

A cikin shekarar 1917, a yunƙurinsa na kai ziyara wani gidan Yari (gidan kaso) da ke Garu, mutane suka jefe shi, wanda aka zargi wata matar Sarki Abdullahi wacce kuma ‘ya ce ga gidan sarautar Kano, da haɗa wannan tawayen.

Faruwar wannan lamari ta saka su Turawa suka tozarta Ɗan-Lawan ta hanyar tuhumarsa da gajiyawa wajen gudanar da mulki da kuma ta’annuti da dukiyar jama’a. Saboda haka aka Tsige shi.

Haka nan shi ma Sarki Abdullahi ta nasa ɓangaren suka tuhume shi da tunzura jama’a su yi wa hukuma bore, saboda haka sai shi Rasidan na wannan lokacin Mr. W.F. Gowers ya yi amfani da wannan dama wajen tsige shi a shekarar 1919.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

Share
Tweet

Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

Share
Tweet

Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub