Hakimin Dutse Haladu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Haladu Ɗan Suleman 1903 – 1910 (Hakimi)


Gabatarwa

Haladu Ɗan Suleman shi ne hakimin Dutse na farko. Bayan da Turawa suka ci Kano da yaƙi, sannan kuma suka naɗa Wamban Kano Muhammadu Abbas a matsayin sabon Sarki Kano (1903 – 1919), sai shi kuma sabon sarkin ya naɗa Haladu Ɗan Suleman wanda yake ɗan ƙanwarsa ne a matsayin hakimin Dutse.

Wannan naɗi na Sarki Haladu, ya haifar da ɓaraka tsakanin Yalligawa, inda suka kalli naɗin kamar cin fuska a gare su, kasantuwar an ɗauki ƙaramin ƙaninsu an yi masa wannan sarauta. Sannan kuma a ta ɗaya ɓangare an ƙasƙantar da sarautar Dutse baki ɗaya. Saboda haka  sai suka yiwa wannan naɗi tawaye.

Ɗan’iyan Dutse, Muhammadu Hamawabi, wanda shi masu naɗin Sarkin Dutse suka zaɓa, da sauran ‘ya’yan sarki, su suka bijirewa wannan naɗi, wanda daga baya shi Ɗan’iya Muhammadu ya yi gudun hijira zuwa Barno, bai sake dawowa Dutse da zama ba har sai da Sarki Haladu ya bar karagar mulki a cikin shekarar 1910.

A tana nasa ɓangaren kuma shi Sarki Haladu, sai ya yi rashin sa’ar samun cikakkiyar karɓuwa daga ɓangaren Turawa, saboda sun kalle shi a matsayin wanda ya gaza wajen tattara kuɗaɗen haraji yadda ya dace, da kuma samar da zaman lafiya a ƙasar ta Dutse.

Rashin samun cikakken goyon baya daga ɓangaren manoma da aka samu a cikin wasu masarautun na Ƙasar Kano, ya saka Turawa rashin jure wannan halin. Saboda haka sai shi Residan Mr. Cargil ya fito da sabuwar hanyar tattara wasu masarautu ƙarƙashin ƙasar hakimi ɗaya, dan ragewa sarakunan Fulani ƙarfin faɗa a ji, da kuma samar da dagatai waɗanda ke kula da doka da oda a wasu yankunan, tare kuma da tattara kuɗaɗen haraji.

Wannan sabon salo da aka fito da shi ya sake ragewa shi Hakimin Dutse daraja da kuma ƙarfin faɗa-a-ji a wannan yanki nasa. A wannan zamani an haɗe masarautar Dutse, Gaya da Jahun waje guda inda suka koma ƙarƙashin kulawar Waziri. Haka nan kuma ta ɓangaren samun kuɗaɗen harajin sai aka yi gamo-da-katar, yawan kuɗaɗen ya ƙaru sosai a cikin shekarar 1906 - 1908. Saboda haka, sai shi Residan Mr. Cargil ya samu ƙwarin guiwar sake karkasa Masarautar Kano zuwa ƙasashen hakimai har guda goma sha huɗu, inda ita Dutse aka sake mai da ita hakimi guda ba tare da haɗin wasu ba. Sai dai, an sake yi mata rassa har guda huɗu waɗanda aka ɗorawa wasu manyan sarakunan Dutse kula da su. Waɗannan sarakuna su ne Madakin Dutse, Sarkin Yaƙin Dutse, Tafidan Dutse, da kuma Makaman Dutse.

A wannan sabon tsarin kuma sai shi Residan ya saka kyautar kaso goma sha biyar zuwa ashirin (15 – 20%) na yawan kuɗaɗen da aka tattara ga kowane hakimi. Hakan nan dai cikin rashin sa’a, a shekarar 1909, sai aka yi fari a yankin Dutse. Wanda wannan ta saka Residan ɗin riƙo. Mr. H.R. Palmer ya tuhumi Sarki Haladu da wasararere da dukiyar al’umma, wanda daga baya aka tuɓe shi daga karagar mulki.

Bayan cire shi daga karagar mulki, sai Hakimin Dutse Sarki Haladu ya yi gudun hijira shi da iyalansa zuwa Kano inda ya rasu a shekarar 1914. Bayan rasuwarsa ya bar ɗansa Muhammadu Inuwa yana sarautar Ciroman Dutse wanda daga baya aka ɗaukaka darajarsa zuwa Sarkin Dawaki Mai Tuta na Masarautar Kano a shekarar 1950 – 1952, a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero Ɗan Abbas (1926 – 1953).

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub