Hakimin Dutse Hamidan

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hamidan Ɗan Ibrahim 1912 (Hakimi)


Gabatarwa

Hamidan Ɗan Ibrahim Bajallige, shi ne hakimin Dutse na uku, sannan kuma Bajallige na farko da ya ɗare karagar mulki bayan zuwan Turawa. Tun kafin zuwa Turawa da Sarkin Dutse Salihu Ɗan Ibrahim (1893 – 1894) ya bar karagar mulki, basu sake samun mulki ba sai a wannan karon, kimanin shekaru 18 kenan.

Wannan Naɗi nasa ya biyo bayan tsige hakiman Yalligawa guda biyu da Rasidan suka yi, saboda haka sai mulki ya juya gidan Jalligawa a wannan karon.

Sai dai, kasancewar dama sarki Hamidan ba mai cikakkiyar lafiya ba ne, sai ya zamana bai iya taɓuka komai ba a zamanin mulkinsa. Tun kafin hawansa karagar mulki ya yi fama da ciwon sukari tsawon shekaru, wanda har ya kai matsayin da ya cinye masa wasu sassan jiki. Saboda haka da aka rantsar da shi, sai abin ya tsannanta. Ya rasu bayan kwana biyar kacal, da naɗa shi a matsayin sabon hakimin Dutse.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub