Sarkin Dutse Ƙetare

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Ƙetar


Gabatarwa

Sarki Ƙetare shi ne ƙaramin ɗan Sarki Tuwai wanda ya zamo sarkin Dutse na biyu. Mulkinsa bai yi tsawo ba. Shi dama mutum ne mai yawan laulayi tun yarintarsa. Ya kasance mai yawan kukan rashin lafiya tun yana ƙarami, a saboda haka ne ma aka yi masa laƙabi da Mai Kuka. Mahaifinsa ya bayyana cewa shan ruwan da ke gudana a yamma da dutsen Asarki shi ne zai warkar da shi, ruwan da daga baya aka riƙa kiransa da suna Kuka wanda ya samo asali daga sunan Sarki Ƙetare. Ya yi mulki na tsawon watanni uku kacal.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub