Sarkin Dutse Natata

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Mamman Natata 1797 – 1799


Gabatarwa

Sarki Mamman Natata shi ne sarkin Dutse na ishirin da bakwai. Shi ɗa ne ga sarkin Dutse Zubairu Tsohon Mutum (1737 - 1797). Shi mutum ne manomi kuma makiyayi. Wato yana noma da kiwo. Saboda haka ya zama mutum mai tarin dukiya.

Sarki Mamman Natata bai saka kansa cikin harkokin farautar bayi da kuma ginin ganuwar gari kamar yadda sarkin da ya gabace shi ya yi ba, shi ya mayar da hankalinsa ne wajen kula da dukiyarsa. Sannan kuma ya ƙarfafi guiwar jama’arsa suka manta da yaƙe-yaƙe suka shagala cikin harkokin sana’o’in gargajiya. Wannan dalili na rashin damuwa da harkar ganuwa ya haifar da rugujewar wasu sassan ganuwar. Ya rinjayi maƙwabtansa ta hanyar tura musu gudunmawar hatsi da kuma dabbobi masu tarin yawa wanda hakan ta hana su afka masa da yaƙi.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub