Shafin Farko

Garaya

Gabatarwa

Garaya abar kiɗa ce da take cikin ayarin kayan kiɗan Hausa wacce ta faɗa rukunin kayan kiɗan tsirkiya. Akan haɗa kiɗan garaya da buta wacce ita kuma ɗaya ce daga cikin kayan kiɗan girgizawa.

Ana yin kiɗan garaya a bukukuwan Hausawa da suka haɗa da bori, girka, bikin shan kabewa, bikin aure da sauransu.

Kiɗa Garaya


Ibrahim Mai Garaya Ungogo a Bakin Aiki

Kayan Kiɗa

Kayan kiɗan garaya sun haɗa da:

  1. Garaya: Ita ce asalin garayar da ake kaɗawa.

  2. Garaya

  3. Butar Caki: Butar duma ce da ake rarake cikinta a zuba ‘ya’yan kurna a cikinta sai a rufe bakinta da tsumma a riƙa girgizawa tana bayar da sauti.

  4. Butar Caki

  5. Wuri: Da shi ake kaɗa garayar da kuma buta; sai dai ita buta shafa ta ake yi da shi.

  6. Wurin Kaɗa Garaya


    Kurin Kaɗa Butar Caki a Tafin Hannu

Kayan Haɗi

Ana haɗa garaya da:

  1. Sanda.
  2. Tsirkiya; a yanzu an fi amfani da lilo.
  3. Ƙoƙo ko butar duma.
  4. Fatar gada ko ta akuya ko ta guza da sauransu.
  5. Alhowa.
  6. Kiɗa Garaya


    Ibrahim Mai Garaya Ungogo a Bakin Aiki

Haɗi

Ana haɗa garaya ta hanyar fafe ƙoƙo ko butar duma. Sannan a samu sanda siriri mai kimanin tsawon zira’in hannun dogon mutum a zura shi cikin ƙoƙon. Sannan sai a kawo jemammiyar fata a rufe dukkan ƙoƙon a haɗe shi da sandar nan a ɗinke a kuma yi masa ƙofa a gefe daga tsakiya. Sai kuma a kawo tsirkiyoyi biyu a ɗauro su daga jikin sandar; ta cikin ƙofar saman ƙoƙon ta hauro ta saman fatar da aka rufa a kan ƙoƙon a ja ta zuwa wuyan sandar a ɗaure su da alhowa (Alhowa jemammiyar fata ce da ake tsaga ta a yi igiya da ita).


Ƙundun Garaya

Manazarta


Tattaunawa da Ibrahim Mai Garaya a Garin Ungogo ta cikin jahar Kano a ranar Lahdi, 2/12/2018.

Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.