A'antawa
Gabatarwa
Kalmar a’antawa, samammiya ce daga a’a, wacce ke da ma’ana ta kore aiki ko wani abu; abin nufi shi ne cewa, tana nuna rashin samuwa ko faruwar wani abu. Misali: Wancan gida ne, wancan ba gida ba ne.
Idan muka lura da jimlar farko “Wancan gida ne”, za mu ga cewa ta nuna samuwar gida a wani bigire da ake iya hangowa. Jimla ta biyu kuma “Wancan ba gida ba ne”, ta kore samuwar gidan da ake magana a kansa. Saboda haka wannan jimla ta biyu ta a’antar da jimlar farko.
Ga kuma wani misalin a cikin magana: Ado, kai ne ka zubar da wannan ruwan? A’a. Wannan kalma da Ado ya bayar da amsa da ita, ita ake ɗafawa “ntawa” a goshinta sai ta zama a’antawa duk kuwa da cewa tushen/saiwar kalmar ita ce a, ta zama a’a, sannan aka yi mata ɗafiyar ntawa a goshi ta koma a’antawa.
Ƙa’idojin A’antawa
Ƙa’ida ita ce abar da ke jan ragamar kowane lamari ya tafi yadda ya kamata sannan kuma bai ɗaya a kowane bigire sannan kuma a koda wane lokaci. A’antawa ma ba a barta a baya ba.
Kalmomin a’antawa: Ana a’antar da zance da kalmomin ba, kada, da maras.
A’antawa da Lokutan Aikatau
Ana amfani da a’antau ba ta sigar ba……ba wajen a’antar da lokutan aikatau masu zuwa:
Shuɗaɗɗen Lokaci: Shi ne aikin da ya wuce. Misali:
- Kura ta wuce.
Ba kura ce ta wuce ba. - Ka karanta.
Ba ka karanta ba. - Sun sayar.
Ba su sayar ba.
Lokaci na yanzu: Shi ne aikin da ke faruwa a lokacin da ake magana. A wannan yanayin ana amfani da a’antau ba, sannan sai kuma wakilin suna ya biyo bayanta. Saɓanin yadda muka gani a baya. Misali:
- Suna magana.
Ba sa magana. - Yana cin abinci.
Ba ya cin abinci.
Sababben lokaci: Shi ne aikatau ɗin da ke nuna aikin da aka saba yi. Da ba………ba ake a’antar da shi. Misali:
- Kukan zo tare.
Ba kukan zo tare ba. - Yakan wanke hula.
Ba yakan wanke hula ba. - Takan kula shi.
Ba takan kula shi ba.
Lokaci Na Gaba Na I: Shi ne lokaci mai zuwa nan gaba. Ana a’antar da shi da ba………ba. Misali:
- Za su tafi.
Ba za su tafi ba. - Za mu hau jirgi.
Ba za mu hau jirgi ba. - Za ka mayar.
Ba za ka mayar ba. - Za ta dafa tuwo.
Ba za ta dafa tuwo ba.
Lokaci Na Gaba Na II: Lokaci mai zuwa. Ana a’antar da shi da ba…..ba. Misali:
- Taa rubuta shi.
Ba taa rubuta shi ba. - Maa nuna masa.
Ba maa nuna masa ba.
Umarni: Ita ce kalmar aikatau da ke nuna umarni. Ana a’antar da ita da a’antau kada. Misali:
- Yi dariya.
Kada ka yi dariya. - Fice daga nan.
Kada ki fice daga nan. - Ku tafi.
Kada ku tafi.
Siffa
Ana a’antar da siffofin mai da masu ta hanyar juya su zuwa maras da kuma marasa. Kalmar mai, tana siffanta namiji ko mace mamallaki wani abu guda ɗaya. Jama’unta ita ce masu. Misali:
- Mai mutunci
Maras mutunci. - Masu mutunci
Marasa mutunci. - Mai hankali
Maras hankali. - Masu hankali
Marasa hankali.
Ɗauraya
A’antawa ita ce kore abu. Kalma ce da ta samo asali daga a’a, wacce aka yi wa ɗafiya a goshi da ntawa. Ana amfani da kalmomin ba, kada, maras da marasa wajen a’antar da zance. Ita ba, tana da sigogi guda biyu; ba da take aiki da lokaci na yanzu, sai kuma ba…………ba, wacce take aiki da shuɗaɗɗen lokaci, lokaci na gaba I da II, da kuma sababben lokaci. Kada, tana a’antar da umarni. Daga ƙarshe kuma, sai maras da marasa da suke a’antar da siffa a jinsin namiji da mace, tilo da jama’u. Marasa, ita ce take ɗaukar jama’u.
Manazarta:
Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.
Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.
Takarda/Muƙala
- Gudunmmawar Harshe...
- Matsayin Sana'o'i...
- Tasirin Mawaƙan Baka...
- Jiya da Yau...
- Gudunmawar Shafuka..
- Bitar Ma'anar Kalmar 'Hausa' ...
- 'Fathers' and 'Mothers' in Hausa...
- Friendship Requires Visits...
- Indigenous Languages...
- Dialectal Variation...
- Ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗan Baka
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da Ƙoƙi da Kantu
- Gizo da Ɗanrago...
- Gizo Ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da Ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da Ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ɓarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Bukukuwa
Wasanni
Karin Magana
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Kayan Kiɗan Hausa
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin