Adabin Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Adabin Hausa


Gabatarwa

Wannan kalma ta ‘adabi’, ararriyar kalma ce daga Larabci (Ɗangambo, 1984; Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa, 1992; Junaidu, da ‘Yar’aduwa, 2002). Ɗangambo (1984), ya ce: “Ma’anarta ta Larabci ita ce “halin ɗa’a, fasaha, ƙwarewa”. To, amma a Hausa, har ma a Larabcin, wannan kalma, tana nufin abubuwan da suka shafi al’adu da rayuwa da fasaha na al’umma; wani lokaci da kuma nazarinsu. A taƙaice, muna iya cewa, adabi, shi ne mudubi ko hoton rayuwa na al’umma. Wannan, ya ƙunshi yadda al’adunsu, ɗabi’unsu, harshensu, halayyar rayuwasu, abincinsu, tufarsu, makwancinsu, hulɗoɗinsu, tunaninsu, da ra’ayoyinsu da sauran abubuwan da suka shafi dabarun zaman duniya don ci gaba da rayuwa; kai har ma da abubuwan da suka shafi mutuwa”.

Adabi shi ne madubin rayuwar al’umma. Misali, idan kana son sanin cikakkiyar al’ummar Hausawa, to ka karanta adabinta. Shi zai bayyana maka komai game da rayuwar Bahaushe kamawa tun daga haihuwa har zuwa mutuwa.


Dukuru, mazubi ne da ake ajiye kayayyaki a cikinsa.

Rabe-Raben Adabin Hausa

Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce ya kasu zuwa:
  1. Adabin gargajiya (Adabin Baka).
  2. Adabin zamani (Rubutaccen Adabi).

Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), sun ambace shi da:

  1. Adabin Gargajiya.
  2. Rubutaccen Adabi.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), suka ce:

  1. Adabin Baka.
  2. Rubutaccen Adabi.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da “yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandare. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub