Adabin Gargajiya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gabatarwa

Tun kafin zuwan Larabawa sannan kuma daga baya Turawa ƙasar Hausa, akwai hanya da Hausawa ke bi wajen gudanar da rayuwarsu da kuma isar da saƙonni ta kowace fuska kamawa tun daga karantarwa, zaburantarwa, nishaɗantarwa, gargaɗantarwa, da sauransu. Dukkan waɗannan abubuwa akan yi su ne a gargajiyance da baki. Misali, akan bi hanyar waƙa wajen zaburantar da mutum kamar mafarauta, ‘yan’dambe da sauransu. Haka nan akan bi ta hanyar tatsuniya wajen koyawa yara kyawawan ɗabi’u ta hanyar labarai a cikin tatsuniyar.

Saboda haka wannan tsohuwar hanya, ta karantarwa da sauransu da baki ake yinta, ba a rubuce ba. Wannan dalili ne ya saka masana suka kira ta da Adabi amma na gargajiya. Wannan rubutu da ka ke karantawa, nan akalarsa ta karkata. Bayan sunan Adabin Gargajiya kuma akan kira shi da Adabin Baka. Saboda haka, a wannan rubutun, duk gurin da aka ci karo da kalmar Adabin Gargajiya, ko Adabin Baka, to suna nufin abu guda ne.

Ma’anar Adabin Gargajiya

Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce, “adabin gargajiya, shi ne adabin da Hausawa suka gada daga kaka da kakanni”.  Amma Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), sun kalle shi a matsayin nau’in adabi wanda ke ɗauke da zantuttuka gajeru ko dogaye na hikima waɗanda ke koyar da wasu darrusa.

Kenan, adabin baka ko adabin gargajiya, adabi ne da yake wanzuwa ta hanyar magana; da baki ake isar da shi haka nan ma taskace shi. babbar hanyar isar da shi ita ce kunne ya girmi kaka. Idan ana son nazartar rawuyar Bahaushe ta wannan sigar sai a duba abubuwan da ke ƙunshe cikin wannan buhu na Adabin baka. Yana da rassa ko rabe-rabe.

Rassan Adabin Gargajiya

Adabin baka yana da ajujuwa ko rassa da dama, Farfesa Ɗangambo (1984), ya karkasa shi a dunƙule kamar haka:
  1. Tatsuniyoyi da labarai.
  2. Almara da wasa ƙwaƙwalwa.
  3. Ƙissa da hikaya.
  4. Waƙoƙi da kaɗe-kaɗe.

Su kuwa Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), sai suka karkasa shi kamar haka:

  1. Zube: Ya ƙunshi tastuniya, almara, hikaya, ƙissa, tarihi, tarihihi, labari, barkwanci, da sauransu.
  2. Waƙa: Ta ƙunshi waƙoƙin baka, kaɗe-kaɗe, bushe-bushe, tumasanci, roƙon baka da sauransu.
  3. Azancin magana: Ya ƙunshi Karin magana, salon magana, kacici-kacici, zaurance, karya harshe/ƙarangiya, waskiya, baƙar magana, ba’a, zambo, sara, kirari da sauransu.

Bayan waɗannan rabe-rabe da muka gani daga waɗannan fuskoki guda biyu, haka kuma abubuwan da suka shafi sana’o’i, al’adu, bukukuwa, da sauransu, suma suna cikin wannan aji na Adabin Gargajiya ko Adabin Baka.

Amfanin Adabin Gargajiya

  1. Koyar da tarbiyya: Adabin baka hanya ce da kaka da kakanni ke amfani da ita wajen koyawa yara tarbiya cikin hikima ta hanyar magana kodai kai tsaye ko kuma cikin labari.
  2. Taskace al’adu: Ta hanyar adabin baka Bahaushe ya ke taskace al’adun gargajiya.
  3. Fito da yanayin zamantakewa: Ta hanyar adabin gargajiya Bahaushe ya ke sanar da jama’a yadda yanayin zamantakewarsa ya ke.
  4. Koyar da Fasaha da kuma Taskace ta: Ta hanyar adabin gargajiya na gaba suke koyar da ‘yan baya irin fasahar da Allah ya hore musu, kamar idan muka duba yanayin zamantakewar Bahaushe za mu ga a cike take da darrusa a ko da wane lokaci kuma a ko’ina za ka ga yara suna ɗamfare da manya suna koyon abubuwa.
  5. Taskace tarihi da kuma yaɗa shi: Ta hanyar adabin gargajiya ne tarihin al’ummar Hausa ya ke wanzuwa, musamman ta hanyar nan da aka fi sani da kunne ya girmi kaka.
  6. Nishaɗantarwa: Ta hanyar adabin gargajiya Bahaushe ya ke nishantar da kansa. Waƙoƙi, tatsuniya, kaɗa-kaɗe, barkwanci, wasanni, da bukubuwa da sauransu, dukkan waɗannan suna daga cikin hanyoyin da Bahaushe ya ke bi yana nishaɗantar da kansa ko dai a lokutan bukukuwa ko kuma a lokacin zama haka kawai.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub