Almara

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Almara


Gabatarwa

Almara ƙirƙirarren labari ce wanda faruwa ko aukuwar abin da labarin ke ƙunshe da shi ya ke da wahala. A cikin irin waɗannan labaru akan kawo wata matsala mai sarƙaƙiya, sai a bayar da labarin sannan a tambayi masu sauraro warwarar wannan matsala, ko kuma a bayar da labarin kawai da nishaɗantarwa ta hanyar bandariya. Almara kafa ta nishaɗantarwa, ɗabe kewa, kaifafa tunani, da sauransu.

Rabe-Raben Almara

A dunƙule, masana harshen Hausa sun kasa almara zuwa gida biyu:
  1. Almarar Wasa Ƙwaƙwalwa: ita ce almarar da ke ɗauke da labarin da ke ɗauke da matsalar da bayan an gama bayar da shi za a buƙaci masu sauraro su warware matsalar.

    Misali, wata rana, wata budurwa ta je zance wajen saurayinta da ya ke wani gari. Da suka gama zance, dare ya yi, sai ya tafi zai raka ta. A tsakanin waɗannan garuruwa guda biyu, akwai wani kogi. Da suka isa bakin wannan kogi, sai saurayin ya ce budurwar ta dakata, ya iya ruwa, shi zai fara haura kogin ya ɗauko kwale-kwale don ya haye da ita. Sai ya shiga ruwa, sai da ya je tsakiyar ruwan, sai wani ƙaton kada ya biyo shi zai kama shi, da ƙyar ya samu ya haye. Bayan ya haye, sai ya hango kura ta rugo da gudu za ta cinye wannan budurwar tasa. To, wai idan kai ne wannan saurayin ya zaka yi? Za ka shigo ruwa kada ya cinye ka ne, ko kuwa za ka tsaya kura ta cinye budurwar taka?

  2. Almarar Raha: almara ce da ake yin ta ta hanyar bayar da labarin bandariya, wacce kuma ba ta ɗauke da wata matsalar da a ƙarshe za a nemi mai sauraro ya warware ta.

Akwai kamanceceniya tsakanin almara da tatsuniya. Sai dai, babban abin da ke bambanta tsakaninsu su shi ne cewa, an fi gina almara da sunayen mutane, wato ba a cika gina zunzurutun labarin almara da sunayen wasu halittu zalla ba batare da mutum ya shigo ciki ba.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da 'Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandare. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub