Aure a Kasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Aure a Kasar Hausa


Gabatarwa


Taro Addu'ar Ɗaurin Aure

Aure alaƙa ce ta halascin zaman tare tsakanin namiji da mace (Habib, Usman, da Rabi’u, 1982). Ana yin aure domin abubuwa da dama, daga ciki akwai kariya daga zina, samun nutsuwa da kwanciyar hankali, samawa abin haihuwa (abin da aka haifa wato ɗa ko ‘ya) mutunci, da sauransu.

Akan samu bambance-bambancen al’adu daga yanki zuwa wani yankin a ƙasar Hausa. Amma akwai gama-garin abubuwa, waɗanda ko’ina ana yinsu.

Neman aure

Akwai matakai da yawa da ake bi wajen neman aure a Ƙasar Hausa.

 1. Matakin Farko shi ne bayyana so. Wanda ake yinsa ta hanyoyi da dama. Amma mafiya shahara a ciki su ne:
  • Hanya ta farko ita ce saurayi ya ga budurwa yana so. Idan haka ta faru to ba shi zai yi mata magana kai tsaye da kansa ba, zai samu babban abokinsa wanda suka amincewa juna ya sanar da shi, idan shawararsu shi da abokin nasa ta yi daidai, to shi abokin nasa ne zai yi wa budurwar magana. Ko kuma wani daga cikin su (saurayin ko abokin nasa), ya samu ƙawar budurwar ya gaya mata ita kuma ta isar da saƙon zuwa ga wacce ake so. Idan aka samu dacewa a tsakaninsu, to shi ke nan.
  • Hanya ta biyu kuma ita ce ta hanyar kamu: Kamu a neman aure shi ne idan iyayen yaro sun ga wata yarinyar da aka san gidansu mutanen kirki ne, sai su ce muna kamu ko mun yiwa wane kamu. Ta irin wannan sigar ce ake samun abokai maza ko ƙawaye mata su haɗa ‘ya’yansu aure.
 2. Kyauta:

  Kyauta ita ce mataki na biyu a cikin neman aure. Ita wannan kyauta shi mai nema ko iyayensa ne ke kai kyautar gidan matar da za a nema. Daga nan kuma sai iyayen yarinya su bada dama shi mai nema ya fara zuwa ko dai kai tsaye gidan matar da za a nema ko kuma gidan wasu makusantan iyayen nata waɗanda ake kyautatawa zaton ba za su bari wani abu na lalata ya shiga tsakanin saurayin da budurwar ba.

 3. Lefe

  Lefe shi ne mataki na uku na neman aure. Lefe kayayyaki ne da ake haɗawa da suka shafi tufafi da kayan kwalliwa gwargwadon ƙarfin mai nema, a zuba su cikin lefe, daga baya ya koma fantimoti, ko kwalla ko akwatu. A wannan zamanin na yanzu kuma akwatu mai taya, a kai gidan su yarinyar da ake nema. Yawanci mata daga ɓangaren mai nema su suke kai waɗannan kayayyaki.

  A zamanin baya, akan tara waɗannan kayan lefe na mutane da yawa, gwargwadon farin jinin yarinya. Daga ƙarshe kuma sai a zaɓi mutum ɗaya a aurar da ita gare shi.

 4. Baiko

  Baiko shi ne tabbatarwa da wanda za a baiwa yarinya da aure cewa an bashi. Akan raba ɗan abin masarufi kamar irin su alewa da sauran su ga jama’a; musamman makusantan saurayin da budurwar, domin su sheda cewa an tsayar wa da yarinya mijin aure.

 5. Saka Rana ko Tsayar da Rana

  Tsayar da rana ko saka rana, al’ada ce da ake ɗaukar wasu kayayyaki daga gidan mai neman aure, zuwa gidan wacce ake son aura, daga nan sai dukkan ɓangarori biyu su tsayar da wani lokaci mai zuwa a matsayin ranar da za a haɗu a ɗaura aure. Daga cikin irin kayayyakin da ake kaiwa akwai goro, alawa (minti), tabarma, kuɗi, da sauransu waɗanda kan bambanta daga guri zuwa guri.

Ɗaurin aure

Ana ɗaura aure a Ƙasar Hausa ta hanyar tara jama’a a ƙofar gidan mahaifin yarinya ko kuma waliyinta. Kayayyakin da ake tanada sun haɗa da:

 1. Sadaki, kuɗi ne waɗanda iyayen yarinya ke ayyanawa a bisa ƙa’idar aure (Habib, Usman, da Rabi’u, 1982).
 2. Waliyayyai: Mutane ne guda biyu da ɗaya ke tsayuwa ta ɓangaren yarinya (walin ‘ya mace) da kuma ɗaya da ke tsayuwa ta ɓangaren ango (walin ɗa namiji), waɗanda ke a matsayin wakilan ango da na amarya.
 3. Shaidu, su ne jama’ar da ake tarawa waɗanda ke taruwa don su zama shedar cewa daga wannan rana wance ta zama matar wane.
 4. Goro da kuɗin ɗaurin aure: Shi goro ana rarraba wa dukkan jama’ar da suka taru a wannan waje ne. Su kuma kuɗin akan bawa walin ‘ya mace, malamai masu addu’a, da kuma abokan wasanta maza (kuɗin mijin baya).

Addu'ar Ɗaurin Aure

Yadda ake yi

Bayan jama’a sun taru, gidajen biyu sukan koma gefe su zauna, sai gidan maza (masu nema) su ce, “Mun ga abin da muke so gare ku”. Su kuma sai su mayar musu da tambaya su ce, “Mai kama da me?” Sai gidan miji su sake cewa, “Mata”. Daga nan sai su ɗan yi shiru wai sun yi shawara kenan, sai kuma babbansu ya amsa da cewa, “Mun baku bisa sunna”. Su kuma su ce, “Mun karɓa bisa sunna”. Idan aka gama wannan kuma sai a rarraba goron nan da aka zo da shi. Sannan kuma sai a koma ɓangaren liman shi kuma ya yi huɗubar ɗaurin aure sannan ya ce na ɗaura auren wance da wane bisa sadaki kaza, naƙadan ba ajalan ba. Idan kuma ajali ne sai ya ce, ajalan ba naƙadan ba. Sannan ya ci gaba da cewa, “Ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, muhalli da koya addini suna kan wane ɗan wane, jama’a kun shaida?” Sai a amsa masa da cewa, “I, mun sheda”. Za a maimaita wannan har sau uku. Daga nan kuma sai liman ya yi addu’a sannan sai a sallami kowa ya kama gabansa.

An Kammala Ɗaura Aure

Manazarta:


Habib A., Usman I.M. da Rabi’u M.Z. (1982). Zaman Hausawa bugu na Biyu, don makarantun gaba da firamare.

Ibrahim M., Yahaya I., da Bello D. (1982). Hausa Custom. Northern Nigerian Publishing Compnay, Zariya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da 'Yar'aduwa T.M (1992). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Qananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Bukukuwa


  Wasanni  Ƙasar Hausa  Musulunci


  Zuwan Turawa


  Tarbiyya


  Kayan Kiɗan Hausa


  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub