Rumbun Ilimi - Daidatacciyar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Daidatacciyar Hausa


Gabatarwa

Daidatacciyar Hausa ita ce Hausar da masana Harshen Hausa suka yarda a yi amfani da ita wajen rubuta Hausa. Da irinta ake amfani a dukkan tsangayu da sashinan nazarin Harshen Hausa a manya da ƙananan makarantu kamawa daga firamare har zuwa jami’a a faɗin duniya. Ita ce Hausar da marubuta littattafai da mawallafa da kafafen yaɗa labaru na duniya ke amfani da ita. Misalin irin waɗannan kafafen yaɗa labaru akwai BBC Hausa, VOA Hausa, FRI, da sauransu. Rumbun Ilimi ma da ka ke karatu a cikinsa, da ita aka yi amfani.

Kenan, kai tsaye muna iya cewa, daidaitaciyyar Hausa, wacce wasu marubutan ke kira karɓaɓɓiyar Hausa, ita ce Hausar da masana Harshen Hausa tun dauri suka haɗu a kan cewa, da ita za a yi amfani wajen yin rubutun Hausa domin samun daidaito.

Wannan kuma saboda akwai kare-karen Hausa da dama, da suka haɗa da Kananci, Katsinanci, Zazzaganci, Dauranci, Sakkwatanci, Aranci, da sauransu. Idan aka ce kowa zai yi rubutu da nasa karin kamar yadda ya ke magana da shi, to abin zai zama babu tsari babu kan-gado, wanda kuma hakan za ta hana samun ƙa’ida.

Muna yi wa mai karatu fatan dacewa.

Ma’anar Daidaitacciyar Hausa

Daidaitacciyar Hausa, ita ce Hausar da masana Harshen Hausa a duniya suka haɗu a kan yin amfani da ita a matsayin rubutacciyar Hausa.

Akwai kare-karen Hausa da dama da suka haɗa da Kananci, Zazzaganci, Katsinanci, Dauranci, Gudduranci, Sakkwatanci, Gobiranci, Aranci da sauransu. Samun wannan kuma ɗaukaka ce ga kowane harshe a duniya. Saboda haka sai aka samu daidaito a tsakanin waɗannan kare-karen Hausa, aka fitar da guda ɗaya rak, ake nazarinsa a makarantu tun daga firamare har zuwa jami’a.

Amfanin Daidaitacciyar Hausa

Babban amfanin daidaitacciyar Hausa shi ne fitar da kari ko salon Hausa guda ɗaya, wanda za a riƙa amfani da ita a tsakanin dukkan sauran karurrukan Hausa. Wannan kuma ya taimaka sosai wajen:

  1. Samar da ƙa’idojin rubutun Hausa.
  2. Samar da Hausar nazari guda ɗaya; abin nufi a nan, shi ne samar da Hausa guda ɗaya wacce ake nazartar harshen da ita.
  3. Sauƙaƙa fahimtar Harshen.
  4. Samar da hanyar rubuta Harshen Hausa guda ɗaya.
  5. Yaɗa Harshen Hausa ta siga ɗaya.

Asalin Daidaitacciyar Hausa

Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (2010), sun ce, “Daidaitacciyar Hausa an gine ta ne daga Kananci”. Sun kafa hujja da zamowar garin Kano a matsayin matattarar jama’a a Ƙasar Hausa da kuma zaman Ɗanhausa (Hans Visch) a garin, wanda shi ne ya fara kafa ƙa’idojin rubutun Hausa.

Ɗauraya

Daidaitacciyar Hausa ita ce rubutacciyar Hausa, wacce ke da ƙa’idojin rubutu da ake amfani da ita a faɗin duniya wajen rubuta Harshen Hausa. Wannan kuma ya bayar da gudunmawa mai gwaɓi wajen samar da daidaitacciyar hanyar rubuta Hausa guda ɗaya rak. An yi amfani da Kananci daga cikin kare-karen Harshen Hausa da ake da su, kasantuwar garin Kano shi ne matattarar jama’a a Ƙasar Hausa da kuma ƙarin zaman Ɗanhausa, wanda shi ya fara rubuta ƙa’idojin rubutun Hausa a garin na Kano.

Manazarta:

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa) Don Masu

Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adelabu Street, Surulere, Lagos-Nigeria.
Jinju M.H. (2007). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company L.T.D., Gaskiya Building, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Uku.
University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub