Gangunan Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gangunan Hausa


Gabatarwa

Ganguna su ne kayan kiɗan da ake bugawa/dokawa/kaɗawa da hannu ko da madoki wanda ka iya zama ice ko waninsa.

A wannan ayari na kayan kiɗan Bahaushe akwai babbar ganga, banga, ba’ala, badujala, bandiri, bango, duman girke, dundunfa, gangi, jauje, kalangu, kanzagi, kanjau, kotso, kuntukuru, kurya, talle, tandu, tambari, taushi, turu da sauransu.

Sassan Jikin Ganga

Idan aka ɗauki ganga a dunƙulenta aka warware ta, za a same ta da wasu sassa waɗanda suka haɗu suka samar da ita. Waɗannan sassa su ne:

  1. Jikin ganga: Shi ne asalin itacen da ake sassaƙewa a yi masa siffa, sannan a fafe cikin. Yawancin gangunan Hausa ana yin su ne da itatuwan ƙirya, kwabre ko kuma marke.
  2. Maɗauki: Igiya ce da ake yin ta da fata ko saƙe. Ana maƙala ta a jikin ganga. Da ita ake rataye ganga.
  3. Fata: Da ita ake rufe bakin dukkan gangunan Hausa. Ana yawan amfani da fatar awaki ko ɗan tayi.
  4. Kirinya/Kambu: Ita ce ɗamarar bakin ganga, wacce ake ɗame fata da ita. Amma a jikin kalangu ana kiranta kambu.
  5. Tsirkiya: Igiya ce da ake yin ta da fata, da ita ake kama kirinyar sama da ta ƙasan ganga. Idan kuma ganga mai baki ɗaya ce, akan yayyanka ƙasan gangar a yi wa tsirkiyar maɗauri.
  6. Zaiga: Wasu suna kiranta da Zaga. Tsirkiya ce siririya da ake giciya ta a tsakiyar bakin ganga; wato tana ratsa saman fatar ne daga tsakiya.
  7. Ƙangu: Fata ce jemammiya wacce ake ɗaure tsakiyar kalangu, ɗan tullo da kuma kanzagi da ita. Ita ce ke fitar da asalin shan kalangu. Wannan ɗauri shi ake cewa matsi ko ɗaurin kalangu.
  8. Nake: Danƙo ne da ake mannawa a tsakiyar fatar wasu ganguna. An samar da wannan danƙo daga ƙaron bishiya. Sai a tauna shi, sannan a liƙa.
  9. Ceba: Ƙarfe ne mai ɗauke da zobban ƙarfe, wanda ake kafa shi a bakin gangar noma.
  10. Awara: Ƙarfe ne da ake ɗame gindin banga ko taushi da shi.
  11. Ido: Ƙofa ce da ake yi a gefen wasu gangunan kamar irinsu dundufa, kuntukuru, tamba, taushi da sauransu, wacce ake zuba mai ta cikinta.

Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.

Tattaunawa da Sarkin Kiɗan garin Alitini, Isma'ila Namarke, a garin Alitini, ƙaramar hukumar Warawa, a Jahar Kano, Najeriya. A ranar 17 ga watan 6, na shekarar 2017.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub