Hausa Iskokai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hausa Iskokai


Gabatarwa

Iska, wata halitta ce da ba a ganinta. Jama’un wannan kalma ta iska, ita ce iskoki ko iskokai. A Hausance kuma a al’adance, Bahaushe yana kiranta da suna ‘mutanen ɓoye’ wato a jimillance ke nan. Abin da ake nufi da wannan, shi ne cewa su iskoki mutane ne da ba a ganinsu. An kira su da mutane saboda misaltawa. Amma, gaskiyar magana ita ce, cewa su halittu ne da ba a ganinsu. Idan kuma suka so bayyana ga mutum, to sukan fito a duk siffar halittar da suka ga dama. Misali, suna iya bayyana a matsayin mutum – kyakkyawa ko mummuna, babba ko yaro, mace ko namiji, sannan kuma a kowace irin ƙabila – ko kuma dabba kowace iri ce, ko tsuntsaye da dukkan nau’o’insu, da sauransu.

A wasu lokutan kuma, yana kiran su da ‘aljanu’ da yawansu kenan, guda ɗaya kuma ‘aljani’. Hakanan ta fuskacin jinsi, mace, ana ce da ita aljana, namiji kuma aljani. Ita kuwa wannan kalma ta ‘aljanu’, kalmar (الْجِنُّ - al-jinnu) ce, wacce ta ke Balarabiyar kalma ce, aka jirkita ta ta koma Bahaushiya. Asalinta kuma shi ne (جِنُّ - Jinnu), ba tare da alu (alif) da lanjaye (lam) ba.

A gargajiyance Bahaushe yana ƙudurce cewa kowane mutum yana da iskoki nasa mafi ƙaranci guda ɗaya wanda suke tare da shi a koda wane lokaci. Har idan shi mutumin ya shiga wani yanayi wanda bai yi wa su iskokin nasa daɗi ba, sukan buge shi. Saboda wannan dalilin ne ma ya saka Bahaushe baya yarda a yi masa abubuwa biyu; na farko, Bahaushe a gargajiyance baya so a tsaya masa a ka (maza da mata), sannan kuma baya so wani ya taɓa masa kai ko ya cire masa hula. Haka nan ma mata ba a taɓa musu kai ko a cire musu ɗankwali haka kawai, wannan, saboda tsoron cewa iskokinsa ko iskokinta za su iya buge shi ko su buge ta.

Rabe-Raben Iskoki

Iskokai sun rabu gida biyu;
  1. Farare: Fararen iskoki a nan suna ɗaukar ma’ana ta halayya ce ba ta launi ba. Su fararen iskoki su ne iskokin da ba sa cutar da mutane. Koda sun shiga jikin mutum basa gusar masa da hankalinsa ko raba shi da wani ɓangaren jikinsa, ko kuma kafa sharaɗin da ya saɓa wa addini kafin su fita daga jikin mutum.
  2. Baƙaƙe: Baƙaƙen iskoki su ne masu baƙin hali, masu tsananin mugunta, waɗanda ke kassara mutum, su shanye masa wani ɓangare na jikinsa, ko ma su raba shi da hankalinsa baki ɗaya. Irin waɗannan iskoki irinsu matsafa ke aiki da wasu wajen yin makaru da sauran ayyukansu na tsafi.

Alamomin Bugun Iskoki

  1. Kururuwa: Wasu lokutan wanda iskoki suka buge shi za a ji yana ta kururuwa, wato yana ta kwarma ihu.
  2. Kuka: Wasu iskokin kuma sukan saka mutum ya yi ta kuka da hawaye ne kawai.
  3. Dariya: Dariya maras iyaka. Haka kawai za a ga mutum ya kama dariyar da ba ta da misali.
  4. Yare: Wasu iskokin kuma sukan saka mutum ya kama yaren da ba nasa ba. Misali, a ji Bahaushe yana Indiyanci ko Canisanci, ko Ingilishi, ko Yarabanci, ko Larabci, da sauransu.
  5. Tsirara: Wasu iskokin kuma sukan saka mutum ya kama cire kayan jikinsa, a kowane hali yake kuma a kowane guri yake ba tare da lura da waɗanda ke tare da shi ba. Irin waɗannan iskoki suna daga cikin baƙaƙen iskoki.
  6. Hauka: Hauka a nan na nufin gushewar hankali, wanda ka iya zama na wani ɗan taƙaitaccen lokaci ko kuma na dindin. Baƙaƙen iskoki su ke haifar da wannan.

Warkar da Cutar Iskoki

Ana warkar da bugun iskoki a gargajiyance ta hanyar amfani da magungunan gargajiya da suka haɗa da turare, wato hayaƙi. Ana yin turare ne ta hanyar ƙona wata itaciya, ko ciyawa, ko kuma gauraye ko dai kai tsaye a danne maras lafiya a yi masa, ko kuma a ajiye a gurin da yake. Da sauran hanyoyi masu tarin yawa.

Guraren Zaman Iskoki

A gargajiyance, Bahaushe yana ganin cewa, iskoki sun fi zama a guraren da suka haɗa da:

  1. Bishiyoyi: Bahaushe yana ganin cewa tsofaffin bishiyoyi kamar irin su tumfafiya, tsamiya da kuka musamman masu kogo (kuka da tsamiya), ba a raba su da iskoki.
  2. Bakin Ruwa: Iskoki kan zauna su rayu a bakin ruwa da suka haɗa da kogi, fadamar da ruwa ke shekara a cikinta, tsohuwar rijiyar da babu ruwa a cikinta, tsohon kududdufi, da sauransu.
  3. Maƙabarta: Maƙabarta ma na daga cikin guraren zaman iskoki.
  4. Juji: Juji shi ne gurin tara shara. Wannan guri, guri ne na zaman iskoki.
  5. Duwatsu: Kan duwatsu ma matattarar iskoki ne.
  6. Daji: Iskoki kan zauna su rayu a ƙungurmin daji.
  7. Shuri.
  8. Gidan tururuwa.
  9. Bakin Randa.
  10. Kushewa: Kushewa a wannan rubutu tana nufin tsohon garin da mutane suka tashi suka bari wanda ake iya samun sauran buraguzan gine-ginen garin.

Lokutan Zirga-Zirgar Iskoki

Bahaushe ya keɓance wasu lokuta muhimmai guda biyu da yake ganin su a matsayin lokutan da iskoki suka fi yin zirga-zirga. Akwai tsakiyar rana, da kuma tsakiyar dare. Saboda haka, Bahaushe yana taƙaita karakaina a cikin waɗannan lokuta a duk guraren da aka ambata a sama da ma ƙarin waɗanda ba a kawo su ba a wannan rubutun amma kuma suna daga cikin guraren da Bahaushe ya ƙudurce a matsayin gurin zaman iskoki.

Sannan kuma dai Bahaushe baya yin wasu ayyuka a cikin irin waɗannan lokuta da kuma guraren da aka ambata a sama. Daga cikin irin waɗannan ayyuka akwai cewa ba a yin shara da tsakar rana ko daddare, rashin zama a kan dokin ƙofar ɗaki, d.s. wanda ake ganin hakan kuma camfi ne.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

 

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub