Karin Magana II

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Karin Magana II


  1. A tambayi kalwa zaƙin miya, a tambayi barkono a sha labari.
  2. Abokin damo, guza.
  3. Abokin ɓarawo, ɓarawo ne
  4. .
  5. Abun kiriki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake yi.
  6. Aikin da babu lada, a bari a jingine shi.
  7. Allah a baki, amma a zuci sheɗan.
  8. Allah ɗaya, gari banban.
  9. Allah, ya maida ƙoƙo masaki.
  10. Allura, ta tono garma.
  11. An san da wuyan biri, ake ɗaure shi a ƙugu.
  12. An yi gudun gara, an faɗa gidan zago.
  13. An yi min sagegeduwa.
  14. Ba a aikin banza a Kano.
  15. Ba a raba harshe da haƙori.
  16. Ba wahalalle, sai mai kwaɗayi.
  17. Ba wan, ba ƙanin.
  18. Babu maraya, sai rago.
  19. Bashi ga tsuntsu, ba shi ga tarko.
  20. Biri, tumakan banza.
  21. Buƙatar maje hajji, sallah.
  22. Da safe, ake kama fara.
  23. Da zafi-zafi, akan daki ƙarfe.
  24. Daga ganin sarkin fawa, sai miya ta yi zaƙi.
  25. Dalili, mai sa a leƙa gindin surika.
  26. Dodo ɗaya ake yiwa tsafi.
  27. Dogo da hankali, da ce ne.
  28. Duk gautar, ja ce/Kowace gauta ja ce.
  29. Duk kanwar, ja ce.
  30. Duk wanda ya ce wutar kara ta kwana, to ya kwana bai yi barci ba.
  31. Duk wanda ya ce zai haɗiyi gatari, riƙe masa ƙota.
  32. Duk wanda ya sayi rariya, ya san za ta zubar da ruwa.
  33. Duk wanda ya sayi tsintsiya, yasan za ta yi shara.
  34. Duk wanda ya ɗebo da zafi, bakinsa.
  35. Duk ɗan da ya hana uwarsa barci, to shima bai runtsa ba.
  36. Fankan-fayau.
  37. Fitar barden guza.
  38. Ga zara ga wata.
  39. Garin gyaran gira, an tsole idanu.
  40. Goɗiyar sanƙira, a hauki a riga ki tashi.
  41. Haihuwar guzuma, 'ya kwance uwa kwance.
  42. Hali, abokin tafiya.
  43. Hali, zanen dutse.
  44. Hamburin hangun/hamburin hayam.
  45. Hana wani, hana kai.
  46. Holoƙo, hadarin kaka.
  47. Idan juninka sammako, to wani a tafe ya kwana.
  48. Idan maraya ya ji ana yiwa mai uwa faɗa, sai ya kasa kunne.
  49. Idan rana ta fito, tafin hannu bai iya kareta.
  50. Idan wani ya taka rawa aka bashi kuɗi, in wani ya taka duka zai sha.
  51. Ikon Allah, sai kallo.
  52. In da rai, da rabo.
  53. In ta yi ruwa, rijiya in bata yi ba masai.
  54. In za ka faɗi, faɗi gaskiya komai ta ja maka ka biya.
  55. In za ka gina ramin mugunta, gina shi gajere.
  56. Ina ruwan biri da gada.
  57. Iya ruwa, fidda kai.
  58. Jifan gafiyar ɓedu.
  59. Kafi mai kora shafawa.
  60. Kainuwa, dashen Allah.
  61. Kallo hadarin nesa, ya sa an yi wanka da kashi.
  62. Kallon hadarin kaji.
  63. Kanwa, uwar gami.
  64. Kere na yawo, zabo na yawo, wata rana za a haɗu.
  65. Kowa ya ci da mai, kuɗinsa.
  66. Kowa ya ci ladan kuturu, zai yi masa susa.
  67. Kowa ya ci tuwo da ni, miya ya sha.
  68. Kowa ya ci zomo, ya ci gudu.
  69. Kowa ya tuna bara, bai ji daɗin bana.
  70. Kowace ƙwarya, da abokin burminta.
  71. Kulɓa na ɓarna, ana cewa jaɓa ce.
  72. Kura, ga kwaɗayi ga tsoro.
  73. Kura, ga tsoro ga ban tsoro.
  74. Laifin yaro ƙiwa, laifin babba rowa.
  75. Lauje, cikin naɗi.
  76. Mai rabon ganin baɗi.
  77. Mai tarkon tsuntsaye, baya ɗaga kara.
  78. Mai tsoron ta mutu, shi yake maho.
  79. Ƙaiƙayi, koma kan masheƙiya.
  80. Ƙuda, wajen kwaɓayi akan mutu.
  81. Ƙwarya, ta bi ƙwarya.
  82. Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare ya yi hankali.
  83. Ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba.
  84. Sai an gwada, akan san na ƙwarai.
  85. Sata gidan ɓarawo, rance.
  86. Shege, ka fasa.
  87. Ta fi nono, fari.
  88. Ta nan muka faro, kuturu ya ga mai ƙyasbi.
  89. Takunkumi, ya fi ƙarfin bakin kaza.
  90. Tuna baya, shi ne roƙo.
  91. Wake ɗaya, shi ke ɓata gari.
  92. Ya daɓa wuƙa a cikinsa/ya daɓawa cikinsa wuƙa.
  93. Ya ɗebo ruwan, dafa kansa.
  94. Ya yi amai, ya lashe.
  95. Zafin nema, baya kawo samu.
  96. Zakara, bada ƙwaya ka ci tsakuwa.
  97. Zakaranka, raƙuminka.
  98. Zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.
  99. Zuma, ga zaƙi ga harbi.
  100. Zuru, ta ishi ɗan kunya.

BayaKarin Magana I   Gaba Karin Magana III


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub