Karin Magana III

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Karin Magana III


 1. A rina, an saci zanen mahaukaciya.
 2. A yi sha'ani, ɗanbirni ya cuci na ƙauye.
 3. Abun dariya, kunkuru ya yi wa bushiya ƙafa.
 4. Allah wadarai naka ya lalace, raƙumin dawa ya ga na gida.
 5. Allah, ya kawo baƙon da zai ci da ɗan gari.
 6. Amfanin zunubi, romo.
 7. An ce da ido wa ka raina? Ya ce wanda na ke gani yau da kullum.
 8. Ana bikin duniya, ake na kiyama.
 9. Ba cas, ba as.
 10. Babban goro, sai magogin ƙarfe.
 11. Bakin da Allah ya tsaga, ba zai hana shi abinci ba.
 12. Ban ci nanin ba, nanin ba za ta ci ni ba.
 13. Ban ga ta zama ba, an saci ɗan ɓarawo.
 14. Ban sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya.
 15. Baya ganin zalau, sai ya leƙa.
 16. Cikina kwarkwaro, cikina tashiya.
 17. Cil-da-cil, ganin annabin tsohuwa.
 18. Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.
 19. Da mai kama, ake ƙota.
 20. Da sauran rina, a kaba.
 21. Da wuya ta kashe ka, gwara/gwanda daɗi ya kashe.
 22. Duk wanda ya samu rana, sai ya yi shanya.
 23. Duniya, rawar 'yanmata na gaba ya koma baya.
 24. Fankam-fankam, bata kilishi.
 25. Faɗan da ya fi ƙarfinka, mai da shi wasa.
 26. Ga bikin zuwa, babu zani.
 27. Ga fili, ga mai doki.
 28. Gaba kura, baya siyaki.
 29. Gaba ta kai ni, gobarar titi.
 30. Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah.
 31. Garaje, ga dami.
 32. Guntun goro, ya fi babban dutse.
 33. Gurin da ba ƙasa, nan ake gardamar kokawa.
 34. Haka ma arziƙi ne, ka yi baƙo ya kashe ka.
 35. Idan ba a yi sharar masallaci ba, a yi ta kasuwa.
 36. Idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta, shafawa naka ruwa.
 37. Idan ka ga mutum yana shinshina/sinsina takalami, so yake ya ɗauka.
 38. Idan mafaɗin magana wawa ne, majiyinta ba wawa ba ne.
 39. Idan maye ya manta, uwar ɗiya bata manta.
 40. Idan tururuwa ta so lalacewa, sai ta fara gashi.
 41. Ihunka, banza.
 42. Ka ƙi naka dubu/duniya ta so shi.
 43. Kallon kitse, ake yiwa rogo.
 44. Karambanin baƙo, ya shiga yaƙin masu gari.
 45. Kare da kuɗinsa, sai ya sha lahaula.
 46. Karo ɗaya, ko da ƙwai da dutse a yi.
 47. Kasada, cinikin tsuntsu a sama.
 48. Kasuwar da ba a gayyace ba, daɗin ci gare ta.
 49. Komai aka yi da sabara, sai ta yi kere.
 50. Kuturu da kuɗinsa, al-kaki sai na ƙasan langa.
 51. Kwaɗayi, mabuɗin wahala.
 52. Kyautar shigo ɗaka, ka yi kuka.
 53. Kyawun ɗan maciji, banza.
 54. Magana, zarar bunu.
 55. Mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce kanku ake ji, ni wanka na na ke yi.
 56. Mai kamar zuwa, akan aika.
 57. Me ya fi lafiyata, cin tsiren mata.
 58. Mugun nufi, baya kashe ɗan barewa.
 59. Mutum baya ƙin ta mutane, an ce da ɓarawo ya gudu.
 60. Na yi maka ciki, na yi maka goyo!
 61. Na zo kenan, zuwa sojan badaskare.
 62. Ƙaramar danga, daɗin tsallaka.
 63. Ƙuruci, dangin hauka.
 64. Ragon malam, ga kyau ga araha.
 65. Ratsa unguwa, a haifi kamarka.
 66. Ruwa, ya ƙarewa ɗan kada.
 67. Ruwan da ya buge ka/dake ka, shi ne ruwa.
 68. Ruwan da ya tafasa, baya tsoron ƙuna.
 69. Ruwan dare, gama duniya.
 70. Sa'a, ta fi gata
 71. Sa'a, ta fi sammako.
 72. Sa'a, tafi manyan kaya.
 73. Sarki goma, zamani goma.
 74. Sayen biri, ba igiya.
 75. Shiru ka ke ji, malam ya ci shirwa.
 76. So, mai hana ganin laifi.
 77. Ta guntso, za ta fesar.
 78. Ta yaro, kyau take bata ƙarko.
 79. Tauraruwa mai wutsiya, ganinki ba alheri.
 80. Taɓa kiɗi, taɓa karatu.
 81. Tsintacciyar mage, ba ta mage.
 82. Tsuntsu daga sama, gasasshe.
 83. Tusa, ta ƙarewa bodari.
 84. Wanda ruwa ya ciyo shi, in aka miƙa masa takobi sai ya kama.
 85. Wanda ya taka wuta, idan ya ga toka sai yi nesa da ita.
 86. Wari ya ke yi, an ce da makaho ga ido.
 87. Wuce gona, da iri.
 88. Wuce makaɗi, da rawa.
 89. Ɗan gata, masha wuyar wata rana.
 90. Yaushe rabon duniya, da ayya-raye!
 91. Yaro, masomin babba.
 92. Yunwa, ba a mata lahaula.
 93. Zama lafiya, ya fi zama ɗan sarki.
 94. Zuwa da wuri, ya fi zuwa da wuri.

BayaKarin Magana II   Gaba Karin Magana IV


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub