Kayan Izga

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kayan Izga


Gabatarwa

Su ne waɗanda ake kaɗawa ko gogawa. A cikinsu akwai: Gurmi, garaya, kuntugi, molo, kwamsa, goge, komo, kukuma da lasha.

Sassan Jikin Kayan Izga

Kusan waɗannan abubuwa da za  a zayyano, su ne gama-garin sassan jikin abubuwan kiɗa na izga. Ga su kamar haka:

  1. Fata: Da ita ake rufa abin kiɗa.
  2. Izga: Tsirkiya ce, wacce ita ce zaren da ake ɗaurawa daga saman abin kaɗawa zuwa ƙasa. Kuma ita ake kaɗawa da hannu ko da ƙirgi. Saboda haka ma sunan kayan ya samo asali daga nata sunan ake cewa, kayan izga.
  3. Kallabi: Fata ce da ake ɗaure saman tsirkiya a jikin sanda da ita.
  4. Sanda: Itace ne maras kauri sannan kuma ɗan dogo wanda baya wuce zira’i ɗaya da rabi. A jikinsa ake zura ƙoƙon gurmi da sauransu, sannan kuma a ɗaura tsirkiya a jikinsa daga sama zuwa ƙasa.
  5. Farke: Ƙirgi ne, wato busasshiyar fatar saniya ko kuma tsinken gashin ungulu, waɗanda ake kaɗa wasu daga cikin kayan izga da su. Ana kaɗa garaya da komo da farken ƙirgi. Kuntigi kuma da tsinken gashin ungulu ake kaɗa shi.
  6. Ceba: Ƙarfe ne mai ɗauke da zobban ƙarfe, wanda ake kafa shi a bakin gangar noma.
  7. ‘ya’yan baba.
  8. Baka: Itace ne ƙarami ake yi masa sha irin na baka a ɗaura tsirkiya a jikinsa. Ana goga koma, goge, da kuma lasha da shi.

Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.

Tattaunawa da Sarkin Kiɗan garin Alitini, Isma'ila Namarke, a garin Alitini, ƙaramar hukumar Warawa, a Jahar Kano, Najeriya. A ranar 17 ga watan 6, na shekarar 2017.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub