Wasan Kokawa
Gabatarwa
Hoton Kiɗan Kokawa
Kiɗan Kokawa
Kokawa wasa ce da ake yin ta a Ƙasar Hausa, musamman a lokutan kaka. Manoma su suka fi yin wannan wasa. Suna da makaɗansu na musamman. Daga cikin makaɗan maza akwai masu kiɗan kokawa.
Ana gudanar da wannan wasa ne a zamanin baya domin nuna ƙarfi da fasaha ko dabara. Saurayin da ke jin ƙarfinsa ya kai, ko wayonsa ya kai, sai ya yi ɗamara ya tafi fagen kokawa ya je ya tari daidai da shi, su yi ta bugawa har sai an samu wanda ya kada wani.
Manazarta:
Barau A. S. (2007). The Great Attraction of Kano State. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.
Masarautar Dutse (2015). Festivals and Ceremonies in Dutse Emirate. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: www.dutseemirate.com
Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Darrusan Hausa
Bukukuwa
Wasanni
Ƙasar Hausa
Musulunci
Zuwan Turawa
- Turawa
- Ɓullar Turawa
- Zuwan Turawa
- Alfanun Turawa
- Tasgaron Turawa
- Yakin Kano
- Yakin Sakkwato
- Shelar Arewa
- Rubutun Boko
Tarbiyya
Kayan Kiɗan Hausa
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin