Makaɗan Ban-Dariya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗan Ban-Dariya

Gabatarwa

Makaɗan ban-dariya su ne makaɗan da ke yin kiɗa da waƙa domin su saka mutane nishaɗi ta hanyar dariya. Waɗannan makaɗa suna da matuƙar muhimmanci a gun Hausawa. Duk irin maganar da za su gayawa mutum, ba zai tare su da faɗa ba, sai dai kawai a yi dariya har ma a samu wani ya basu kuɗi.

Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce, “Makaɗan ban-dariya, su ne waɗanda sana’arsu ita ce, su ba mutane dariya don a yi raha da nishaɗi a lokacin hutawa, ko shaƙatawa, wurin aiki da sauransu. Su kuma sakamakon wannan abu da suke yi, suke samun ɗan abun masarufi daga jama’a”.

Rassan Makaɗan Ban-Dariya

Akwai hanyoyi mabambanta da waɗannan makaɗa ke bi suna baiwa jama’a dariya. Saboda haka sai aka karkasa su bisa la’akari da irin salon da suke bi suna bada dariya. A cikin makaɗan ban-dariya akwai:
  1. ‘Yan Kama.
  2. ‘Yan Gambara.
  3. ‘Yan Galura.
  4. ‘Yan Ƙoroso.

‘Yan Kama

‘Yan kama makaɗan ban-dariya ne da suke nishaɗantar da jama’a ta hanyar kwaikwayo. Abin da ake nufi da kwaikwayo a nan shi ne yadda su ‘yan kaman ke kwaikwayar waƙoƙin wasu makaɗa, ko karatu ko rawar soja, ko tafiyar wani mutum ko dabba da sauran abubuwa, su juya shi ya koma sigar abinci. Ta wannan hanya su ke baiwa mutane dariya.

Sukan yi shiga ta ɓad-da-kama su saje da manyan mutane. Sukan saka babbar riga da rawani da idan aka gansu ana iya cewa manyan sarakuna ne ko wasu shahararrun malamai. Suna da  ‘yar gangarsu da suke ɓoyewa cikin riga da kuma takobi.

‘Yan kama suna waƙoƙinsu ne ta hanyar kwaikwayon waƙoƙin wasu. Abin da ake nufi da kwaikwayon waƙa a nan shi ne su juya waƙar ta koma wata iri; sukan ɗauki salo da amon waƙar sai su zazzage maganganun da ke ciki su ɗura nasu. Misali, sun juya waƙar Alhaji Mamman Shata ta Dan Allah mata ku yi aure suka mayar da ita Dan Allah mata ku yi koko, kamar haka:

Baitukan Shata
Wai don na ce mata su yi aure,
Kaɗo ya tashi ya tozarta ni,
Har Attaura har Linjila,
Har Alƙur’ani babban kundi,
Ina ayar da kankare aure?

Baitukan ‘Yan Kama
Don na ce mata su yi koko,
Masu kunu suka tozarta ni,
Har Attaura har Linjila,
Har Alƙur’ani babban kundi,
Shin ina ayar da ta kankare koko?
Farfesa Ɗangambo (1984).

Haka nan kuma akwai baituka na waƙar Sarkin Taushin Sarkin Katsina, kamar haka:
Baitukan Sarkin Taushin Sarkin Katsina
Duniya ta yi kyau arziƙi ya yi,
Tun da an bamu mulkinmu mun gode Allah.

Baitukan ‘Yan Kama
Duniya ta yi arziƙi ya yi,
Tun da mun karɓe girki ga matanmu mun gode Allah.

Bayan waƙoƙi kuma sukan yi wani abun duk dan dai su baiwa jama’a dariya. Akwai wani labari da ya shahara mai taken limancin Ɗankama.

Wai an ce wata rana wani ɗankama ya je wani gari sanye da manyan rigunansa da rawani, yana zaune a fadar sarki har lokacin sallah ya yi. Da mai gari ya ganshi cikin shiga irinta kamala, sai ya ce da shi ya shige ya yi musu sallah. Shike nan sai ɗankama ya ja sallah. Bayan da ya kusan gama sallah, a sujjadarsa ta ƙarshe, sai ya daɗe bai ɗago goshinsa daga ƙasa ba, can sai mutane suka ji shi yana cewa, wayyo Allah, sun kama min maƙogwaro, wayyo Allah sun kama min goshi. Da mutane suka ji haka sai kowa ya yi ta-kansa ciki kuma har da mai gari. Can daga baya sai ya fito da gangarsa ya kama kaɗawa yana waƙa, ta haka sai suka gane ɗan kama ne.

Saboda haka a taƙaice dai, su ‘yan kama makaɗan ban dariya ne da suke baiwa mutane dariya ta hanyar kwaikwayar wasu abubuwan da mutane ke yi su mayar da shi abun dariya. Wannan abun kuwa na iya zama waƙa, karatu, tafiya, da sauran abubuwa.

‘Yan Gambara

Su kuma ‘yan gambara makaɗa ne na ban-dariya da suke nishaɗantar da jama’a ta hanyar kiɗa da kuma ba’a. Wato su ba wata tsararriyar waƙa suke yi ba, ba’a ce da habaici da kuma maganganun batsa. Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), sun gutsuro wasu baituka daga cikin irin baitocin ‘yan gambara da ke tabbatar da cewa gambara ba waƙa ba ce kamar haka: “Gambara ba waƙa ba ce, azanci ne yai yawa”.

Mutane biyu ne ke yin kiɗan gambara a tare. Sukan tafi tare suna kiɗa suna kallon junansu suna yiwa junansu ba’a. Kayan da suke sakawa su kansu sun isa su baka dariya. Yawancin lokuta sukan saka matsattun riguna da kuma ɗangalallun wando da ratattakakken takalmi wari dabam-dabam, da kuma zungureriyar hula. Bayan zuwan Turawa kuwa sukan saka wando mai tazuge, da riga shat sannan su zanzare, su yi nektayil da tsumma wasu lokutan kuma suka ƙara da yin belet da igiya.

Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), sun ce asalin sunan gambara daga kalmomin gama kiɗa da bara ne (gama, kiɗa, bara) aka gutsure su suka zama gam-bara. Wato gam daga gama, sai aka cire kiɗa aka yar sannan aka ɗauko bara aka jona sai suka zama gambara. Sannan kuma suka ce asali almajirai ne suke kiɗan gambara.

‘Yan Galura

‘Yan Galura makaɗa ne na ban-dariya, suna kiɗansu ne da butar duma. Sukan samu butar duma su zuba mata tsakuwa a ciki, su tafi suna jujjuyata ita kuma tana fitar da sauti tana kacakar-kacakar. Amma daga baya sun riƙa amfani da gwangwani a madadin butar duma.

Tsofaffi ne ke yin wannan sana’ar. A wasu lokutan ma akan taras da cewa sukan samu yara ‘yan rakiya su yi musu jangora saboda tsufa saboda dalilai na mantuwa, raunin jiki ko raunin gani da sauran larurorin tsufa. Sukan yi shiga irin ta Bahaushe, wato babbar riga da wando da ‘yar ciki. Abin da ke bambanta su da tsofaffin kirki ita ce hula, sukan saka zungureriyar hula. Saboda a gaskiyar magana dama tsofaffin bariki ke yin wannan sana’ar bayan ta gama ƙare musu.

Ba’a, da maganganun batsa, su ne waƙar da ke bin wancan kiɗa nasu. Wato kenan suma ba waƙa suke rerawa ba, suna kiɗa ne sannan kuma suna maganganu na ba’a. Saboda tsufansu wasu lokutan ma har ashare-ashare suke yi musamman ga wanda ya tsokane su ko ya hana su komai.

‘Yan Ƙoroso

Makaɗan ƙoroso suma makaɗan ban-dariya ne. Su ne makaɗan da ke baiwa jama’a dariya ta hanyar kiɗa, waƙa, raye-raye, da kuma tsalle-tsalle. Suna amfani da kayan kiɗan da suka haɗa da sarewa, mara, da kuma ganguna. Sannan suma ba’a da maganganun batsa da shakiyanci su ne abubuwan da ke cikin waƙarsu.

Yawanci masu kiɗan ƙoroso matasa ne. Shigarsu kuma ta haɗa da riga ‘yar shara, hula haɓar kada, akayau, layu, guraye, daga, da sauran kayayyakin shiga irin ta mafarauta ko ‘yan kokawa da sauransu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub