Makaɗan Fada
Gabatarwa
Ana busa algaita
Makaɗan fada su ne makaɗan da basa yiwa kowa kiɗa da waƙa sai jinin sarauta ko wanda yake riƙe da wata sarauta babba kamar irin su sarki, galadima, waziri, hakimai, dagatai, masu unguwanni da kuma irin su sarkin dogarai, da makamantansu. Waɗannan su ne asalin makaɗan fada. Amma yanzu canjin zamani ya saka irin waɗannan mawaƙa yiwa masu kuɗi da kuma masu mulki waƙa (Ɗangambo, 1984).
Makaɗan fada akan kuma kira su da makaɗan sarakuna (Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan, 1992). Suna yiwa sarakuna waƙa ne ba sarautar ba. Yawancin makaɗan fada suna da iyayen gidansu waɗanda su kaɗai suke yiwa waƙa, in ma sun yiwa wani, to sai sun nemi izini a wajen iyayen gidan nasu. Su iyayen gidan nasu su suke ɗaukar dukkan ɗawainiyoyinsu na rayuwa kamawa tun daga abinci, zuwa gurin zama, zuwa sutura, da su da iyalansu.
Wata Tawagar Makaɗan Fadar Kano
Manazarta:
Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.
Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.
Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Kayan Kiɗan Hausa
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da Ƙoƙi da Kantu
- Gizo da Ɗanrago...
- Gizo Ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da Ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da Ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ɓarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Wasanni
Karin Magana
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin