Makaɗan Jama'a

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗan Jama'a


Gabatarwa

Makaɗan jama’a su ne makaɗan da ke yiwa kowa-da-kowa kiɗa da waƙa. Basu da wani takamaiman ubangida sai wanda ya basu. Waɗannan makaɗa sana’ar kiɗa da waƙa ita ce babbar sana’arsu.

Makaɗan jama’a basu da wani keɓantacce guri, ko wani mutum, ko wani lokaci da suke yin waƙarsu. Suna yin waƙarsu a duk gurin da ta samu, ana iya ganin su a fada suna waƙa, misali idan aka ɗauki Alhaji Mamman Shata, ya yiwa sarakuna waƙa, ya yi wa masu kuɗi, malamai, karuwai, da sauransu. Saboda haka, su duk inda ta faɗi, sha ne kawai.

Ga Mamman Shata na Bilkin Sambo mai maƙogwaron zinare a matsayin ɗaya a bakin aiki, a cikin waƙarsa ta Ɗandarman Kano wanda yake basarake ne

Abjadin Hausa

Manazarta:

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub