Makaɗan Mata

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗan Mata


Gabatarwa

Makaɗan mata sune masu yiwa mata kiɗa da waƙa. Su kansu makaɗan matan, mata ne da ake yi wa laƙabi da zabiya, waɗanda ke gudanar da sana’ar kiɗa domin su nishanɗantar da ‘yan’uwansu mata a lokacin bukukuwan aure, suna da makamantansu.

A wajen gudanar da wannan sana’a tasu ta kiɗa, ba kasafai ake samun maza a ciki ba sai dai ɗan abin da ba za a rasa ba. Saboda koda kayan kiɗan nasu ma, za ka ga ba wasu masu nauyi ne sosai ba. Ba su cika amfani da gangaga ba, sukan yi amfani da ƙorai ne wanda ake zuba ruwa a cikin masaki sannan a saka ƙwarya a ciki, ana dokawa. Sauran kayayyakin kiɗan nasu basu wuce shantu, sakaina, acakau, da kuma ludayi ba.

Kiɗan Ƙwarya

Haka nan ma ta fuskacin washi ko kirari, ko yabo, mawaƙan mata, mata ‘yan’uwansu suke yiwa yabo, koda sunan namiji ya fita, yakan fito ne dan ƙara fito da surar su matan da ake wasa danagane su, misali, a cikin waƙar Barmani Coge mai taken A zage zogale tana ambatar sunayen wasu mazaje, daga cikinsu akwai gurin da ta ce:

Allah jiƙan maza a kiyama,
Na tuna na nisa gidan Haruna na Ɗanja,
Ran nan da zani gida na sai takardun Naira a hannu,
Are-re riyalle a zagi zogale.

Kuma na gode, godiya sambarka,
Na ce Hajiya Hajara kin biya kiɗa sai ƙwarya,
Alhajiya Hannatu ta biya kiɗa sai ƙwarya,
Alhajiya Jimmai ta biya kiɗa sai ƙwarya,
Madalla, kuma Allah jiƙan maza a kiyama,
Gidan Haruna na Ɗanja Uban Aminu da Lantai,
Wallahi ko da na je gidan shi roƙo ba a banzata ni ba,
Are-re riyalle a zagi zogale.

Idan muka duba waɗannan baitoci za mu iya fahimtar cewa an yabi wasu mata ne guda uku, Hajiya Hajara, Hajiya Hannatu da kuma Hajiya Jimmai. To, saboda a ƙara fito da waɗannan mata guda uku, akwai buƙatar faɗin inda suke, saboda haka dole sunan mai gidansu ya shigo, wanda a nan, za a fahimci cewa shi mai gidan nasu ma ya rasu, saboda fitowar kalmar Allah ya jiƙan maza a kiyama.

Bari mu rufe rubutun da maganar Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), in da suka ce, “Waɗannan mata ne, zabiyoyi, da kan gudanar da sana’arsu ta kiɗa da waƙa ga mata ‘yan’uwansu. Mafi yawansu ba sa zuwa kai tsaye wajen maza domin su yi masu kiɗa da waƙa, sai dai abin da Hausawa sukan ce, albarkacin kaza, ƙadangare ka sha ruwan kaso. Wato albarkacin matan da aka zo yiwa wasan, akan ɗan sako sunan maigida a ciki a yabi irin gudunmawar da ya bayar”.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub