Makaɗan Sarauta

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗan Sarauta

Gabatarwa

Makaɗan sarauta, makaɗa ne da ke yiwa sarauta kiɗa ba sarakuna ba. Su ne ke buga tamburan gidan sarautar kowace masarauta da ke ƙasar Hausa. Dukkan masarautun ƙasar Hausa, kowace ɗaya tana da takenta ko tambarinta wanda ita kaɗai ake bugawa.

Haka nan ma sarautun gargajiya kowace sarauta tana da kiɗanta. Misali, galadima, wambai, waziri, da sauransu. Kowace sarauta daga cikin waɗannan sarautu tana da nata kiɗan. Duk wanda ke riƙe da ita shi ake yiwa ba sunansa ba. Sannan kuma tun kafin zuwansa kan wannan kujera, su ke yiwa wanda ya gabace shi kiɗa, haka nan ma kuma idan ya tafi, wanda zai biyo bayansa su za su ci gaba da yi masa kiɗa.

Suna amfani da kayan kiɗa da suka haɗa da algaita, tambura, ganguna, da sauran kayayyakin kiɗan sarauta.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub