Rumbun Ilimi - Manya Da Ƙananan Baƙaƙe

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Manya Da Ƙananan Baƙaƙe


Gabatarwa

A dokar rubutun Hausa, akwai wasu gurare da ake fara rubutu da babban baƙi; wato ya zama harafin farko na kalmar babban baƙi ne. harafin kuwa a nan yana iya zama baƙi ko wasali. Misali: B ko A, kowanne harafi ne a cikinsu. Ga wasu daga cikin guraren da doka ta ce a fara rubutu da babban baƙi:

  1. Harafin farko na sunayen Allah. Dukkan gurin da sunan Allah ya zo a cikin rubutu, doka ta ce a fara rubuta shi da babban baƙi. Misali, Allahu, Ubangiji, Assamadu, da sauransu. Amma ba za a rubuta allahu ba, wannan kuskure ne babba.
  2. Harafin farko na sunayen annabawa, mala’iku, littattafai masu tsarki da gurare masu tsarki. Misali, Annabi Muhammadu, Annabi Idirisu, Mala’ika Jibirilu, Alƙur’ani, Linjila, Ka’aba, Masallacin Madina, Uhud, da sauransu.
  3. Sunayen yanka. Misali, Abubakar, Musa, Idi, Maryam, Hauwa’u da sauransu.
  4. Sunayen ƙasashe, jahohi, garuruwa, unguwanni, kasuwanni da sauransu. A nan za a iya la’akari da cewa, dukkan suna na kowace ƙasa ko jaha da sauransu a duniya ya bambanta da na wata, koda kuwa an samu kamanceceniya, to dole a taras sun bambanta. Misali, Najeriya, Nijar Ghana, Kano, Jigawa, Ungogo, Gwaram, Rimin Kebe, Tsangarwa da sauransu.
  5. Sunayen watanni, ranaku, kusurwa da sauransu. Misali, Almuharram, Ramadhana, Lahadi, Juma’a, Gabas, Yamma da sauransu.
  6. Sunayen ƙabilu. Misali, Bahaushe, Bafillace, Balarabe da sauransu.
  7. Wasu sunaye: Akwai wasu sunaye kamar laƙabi, sunan haihuwa; sunan ranar da aka haifi mutum ko garin da aka haifi mutum da makamantansu duk da manyan baƙi ake fara rubuta su. Misali, Nasidi, Tarasulu, Damina, Cinnaka, Maikuɗi, Ɗantala, Ɗanbirni, Namadina da sauransu.

Farkon Rubutu

Dokar rubutun Hausa ta ce idan za a fara rubutu a farkon farawa, to harafin farko ya zama babban baƙi.

Farkon Sakin Layi

Idan za a yi sabon sakin layi a rubutu, to harafin farko ya zama babban baƙi.

Bayan Alamomin (.), (?), (!), (:), (“”)

Dokar rubutun Hausa ta ce dukkan kalmar da za ta biyo bayan ɗaya daga cikin waɗancan alamomi guda biyar, to harafin farko ya zama babban baƙi. Shi kuwa biyo bayan alamar (“Na yi rubutu a nan”) ana nufin idan aka zuba rubutun a ciki, to harafin farko ya zama babba, kamar yadda yake a sama.

Muhallin Ƙananan Baƙaƙe

Dokokin rubuta ƙananan baƙaƙe ababen dunƙulewa ne a cikin faɗin cewa, dukkan kalmar da ta biyo bayan ɗaya daga cikin waɗannan alamomin rubutu, to harafinta na farko ya zama ƙaramin baƙi. alamomin su ne: Baka biyu (), waƙafi (,), waƙafi mai ruwa (;), zarce (…) da kuma kara jirge (/).

Sannan kuma dai dokar rubutun Hausa ta ce ba a gauraya manya da ƙananan baƙaƙe a cikin kalma ɗaya. Misali a rubuta GanYen ƊoRAWA, wannan ba daidai ba ne.

Saboda haka muna iya kammala rubutunmu da cewa, dokar rubutun Hausa ta samar da wasu gurabe da ake rubuta harafin farko na kalmar farko da babban baƙi haka nan ma kuma ƙananan baƙaƙe suna da nasu muhallin da ake son fara rubutu da su. Sannan kuma wannan doka ta hana gaurayen manya da ƙananan baƙaƙe a cikin kalma guda.

Manazarta:

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa) Don Masu

Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adelabu Street, Surulere, Lagos-Nigeria.
Jinju M.H. (2007). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company L.T.D., Gaskiya Building, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Uku.
University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub