Nahawun Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Nahawun Hausa


Gabatarwa

Kalmar nahawu, kalma ce ta Larabci (نحو) aka Hausantar da ita. Nahawu a Hausa na nufin fannin ilimi da ake sanin ƙa’idojin aiki da kalmomi da jimlolin Hausa da shi. Ilimin nahawu shi ya ke baiwa manazarci cikakkiyar masaniyar yadda zai yi hulɗa da kalmomin Hausa ta hanyar sanin guraben da suka dace a jejjefa su domin samun ingantacciyar jimla mai ma’ana.

Wannan fanni na ilimin nahawu, a gaskiyance fanni ne mai matuƙar faɗi da kuma tarin fa’ida. Fahimtar wannan fanni da kuma yin aiki da shi a fagen rubutu, yana fito da rubutu fes, sannan kuma ya mayar da rubutu mai daɗi da sauƙin karantawa.

A fagen nahawu ake sanin kalmomin Hausa sani na haƙiƙa. Bayan an san kalma kuma sai a san a daidai gurbin da ya kamata ta fito a cikin jimla. Abin nufi a nan shi ne cewa, me ya kamata ya zo a gaba da kuma bayan wannan kalma, da abubuwan da suka yi kama da haka nan?

Kenan, kacokaf ɗin ilimin nahawu, ya karkata akalarsa ne kan kalma da kuma jimla, waɗanda kuma su ne suka zama rassan bincike a wannan fanni na nahawu.

Wannan ɗan rubutu da mai karatu yake karantawa, ‘yar gabatarwa ce game da gundarin ilimin nahawu. Sauran abubuwa kuma, sai a nemi kowanne a fannin da ya dace.

Ma’anar Nahawu

Nahawu fanni ne na kimiyyar harshen Hausa wanda ya shafi ginin jimla. A wata ma’anar kuma aka ce, Nahawu shi ne sanin ƙa’idojin harshe (Hausa).

Kenan, daga ma’ana ta farko, za mu fahimci cewa, nahawu, yana bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina kyakkyawar jimla a harshen Hausa. Wanda ita kuma jimla ita ce tushen duk wani rubutu da za a yi a harshen Hausa.

Ita kuma ma’ana ta biyu sai ta yi magana game da sanin ƙa’ida. Kenan, nahawu ne ya ke koya mana ƙa’idojin rubutu a harshen Hausa. Ta wannan hanya mu ke sanin matsayin kalma, abin nufi shi ne cewa a wane ajin kalmomi wannan kalma ta faɗa, sannan ta yaya za a saka ta a cikin jimla? Da sauransu.

Rassan Nahawu

Bisa lura da waɗancan ma’anoni guda biyu da aka zayyano a sama, za mu iya cewa nahawun Hausa yana da rassa guda biyu:

  1. Kalmomi: Shi ne reshen nahawu da ya ɗamfaru da sanin ilimin kalmomi da sauran abubuwan da suka rataya da su.
  2. Jimla: Reshe ne na nahawu da ya ke magana a kan gina jimla da sauran abubuwan da suka danganci jimla.

Daga abin da ya gabata, za mu fahimci cewa kalmar nahawu, an aro ta ne daga Larabci aka Hausantar da ita kuma ta ke ɗaukar ma’anar ilimin kimiyyar harshe da ya ɗamfaru da ginin jimla, da kuma wata ma’ana da take cewa nahawu shi ne ilimin ƙa’dojin harshe. Wannan fanni na nahawu yana da rassa guda biyu; kalmomi, wanda ke magana game da kalmomin Hausa da kuma jimla wanda ke magana akan abubuwan da suka shafi ginin jimla da sauransu.  

Manazarta:


Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub