Bayanau
Gabatarwa
Bayanau kalmomi ne da ke yin ƙarin bayani game da aikatau. Wannan bayani da suke yi shi ya ke fito da aikin a fili. Sukan faɗi gurin da aka yi aikin, lokacin da aka yi aiki ko kuma yadda aka yi, ake yi ko za a yi aiki.
Ma’anar Bayanau
Masana suka ce, kalma ce da ke yin ƙarin bayani game da aikatau a cikin jimla. Wato kenan, wannan kalma, ita ce fitilar da take haskaka aikatau a ganshi a fahimce shi.
Rabe-Raben Bayanau
- Bayanau na wuri.
- Bayanau na lokaci.
- Bayanau na yanayi.
Bayanau na Wuri
Shi ne kalmar da ke bayyana gurin da aka aikata aiki, ko za a aikata ko kuma ake aikatawa. Kalmomi irin su nan, can, gefe, gaba, baya, ƙasa, sama, kusa, nesa, daf, gabas, yamma, da sauransu, duk bayanau ne na wuri. Misali:
- Yana zaune a kan kujera.
- Ta zauna daf da mijinta.
- Ya ajiye tamola a ƙasan teburi.
- Yana noma a gabas da gari.
- Tafi can ka zauna.
Bayanau na Lokaci
Shi ne kalmar da ke yin bayani game da lokacin da aka aikata aiki, ko za a aikata, ko kuma ake aikatawa. Kalmomi irin su jiya, yau, ɗazu, yanzu, gobe, baya, baɗi, dare, rana, safiya, watan mai kamawa, damina, rani, da sauransu, duk bayanau ne na lokaci. Misali:
- Habu ya dawo jiya.
- Na ji wani ihu cikin dare.
- Ai yaron baɗi zai gama karatu.
- Ɗazu ya tafi kasuwa.
- Noman damina abu ne mai riba.
Bayanau na Yanayi
Shi ne kalmar da ke yin bayani game da yadda aka aikata aiki, ko za a aikata aiki, ko kuma ake aikata aikin. Kalmomi irinsu da sauri, a hankali, a fusace, a gigice, a guje, da sauransu, duk bayanau ne na yanayi. Misali:
- Garba ya iya tuƙi a hankali.
- Yaron ya wuce da sauri.
- A guje yake tafiya.
- Shi da yake magana a gigice, ai ba za a fahimci me yake cewa ba.
- A fusace ya zo nan.
Bayanau, kalmomi ne da ke yin bayanani game da aikatau a cikin jimla. Bayanau ya rarrabu zuwa bayanau na wuri wanda ke bayyana wurin da aka yi aiki, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aikin. Sai kuma bayanau na lokaci, wanda ke bayyana lokacin da aka yi aikin, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aiki. Haka nan kuma akwai bayanau na yanayi, wanda shi kuma nuni yake zuwa ga yadda aka aiwatar da aikin, ko za a aiwatar ko kuma ake aiwatar da aikin.
Manazarta:
Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.
Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.
Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.
Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria
Nahawun Hausa
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da ƙoƙi da Kantu
- Gizo da ɗanrago...
- Gizo ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ƙarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Wasanni
Karin Magana
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin