Rumbun Ilimi - Rubutacciyar Waƙa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Rubutacciyar Waƙa


Gabatarwa

Waƙa, wata hanya ce ta isar da saƙo, tana da matuƙar tasiri a harkar adabi. Hanya ce mai sauƙi wajen isar da saƙo kuma cikin nishaɗi. Akwai waƙa da ake rerewa haɗe da kiɗa, akwai kuma rubutacciyar waƙa wacce ake kira waƙe. Wannan rubutun da mai karatu ke karantawa, a kan ta biyun zai yi magana.

Ma’anar Waƙa.

A sauƙaƙƙiyar Hausa, ana iya siffanta waƙa da aunanniyar magana, kamar yadda ya zo a Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002). Ita rubutacciyar waƙa, rubutata ake yi koma da za a rera ta daga baya (Ɗangambo, 1984), sannan kuma tana da ma’auni da sai ta hau kansa kafin ta zama cikakkiyar waƙa.

Rabe-Raben Rubutacciyar Waƙa

Masana sun kasa ta zuwa kashi biyu:
 1. Waƙoƙin ƙarni na goma sha tara.
 2. Waƙoƙin ƙarni na ishirin.

Farfesa Ɗangambo (1984), Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), na daga cikin jerin masanan da suka yi tarayya a kan waɗannan rabe-rabe na rubutacciyar waƙa.

Waƙoƙin Ƙarni na Goma sha Tara

Su ne waƙoƙin farko da aka fara rubutawa a adabin Hausa. Waɗannan waƙoƙi an rubuta su ne cikin rubutun ajami da Shehu Usmanu Ɗanfodiye da almajiransa suka rubuta.

Waƙoƙin Ƙarni na Ishirin

Su ne waƙoƙin da aka rubuta su bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Waɗannan waƙoƙi rukuni biyu ne; rukunin farko su ne waɗanda aka ci gaba da rubuta su a cikin ajami kamar irin waƙoƙin sarkin Zazzau Aliyu Ɗan Sidi, da waƙoƙin Aliyu Namangi, da sauransu. Sai kuma rukuni na biyu waɗanda aka rubuta su da Hausar boko. A wannan rukuni akwai mawaƙa irin su Sa’adu Zungur, Mu’azu Haɗeja, da kuma Abubakar Ladan.

Tarihin Rubutattun Waƙoƙi

Daga abin da ya gabata na rabe-raben rubutattun waƙoƙin Hausa, muna iya cewa, an fara rubuta waƙa ne cikin harshen Hausa a ƙarni na goma sha tara zamanin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo domin wa’aztarwa. Kuma wannan magana tana iya zama mai ƙarfi idan muka ƙarfafe ta da hujjoji. Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), suka ce, “Rubutacciyar waƙa ta samo asali ne daga Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, wato a cikin ƙarni na goma sha takwas zuwa ƙarni na goma sha tara”. Sai kuma Farfesa Ɗangambo (1984), da ya ce, “Kamar yadda tarihi ya nuna, rubutattun waƙoƙi na Hausa, sun fi samuwa ne a ƙarni na 19. Ko ma da an sami rubutattun waƙoƙi kafin ƙarni na 19, to, kaɗan ne. Bisa haƙiƙa ma, waƙa ɗaya ce wadda dai ake da ita a yanzu, ake zaton an yi ta a ƙarni na 17/18, wato “Waƙar Badar”, ta Wali Ɗan Masani na Katsina”.

Nazarin Rubutattun Waƙoƙi

A taƙaice, mai nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa zai lura da abubuwa kamar haka:
 1. Jigo: Shi ne saƙon da aka gina tubulin waƙar a kansa. Abin nufi, saƙon da ake son isarwa a waƙar. Akan gina waƙoƙi a kan jigo da suka haɗa da wa’azi, yabon Annabi da waliyayyai, soyayya, gargaɗi, siyasa, da sauransu.
 2. Zubi da Tsari/Salo: Ana rubuta waƙa ne a layi-layi wanda ake kiran kowane layi guda ɗango. Waɗannan layuka (ɗangwaye) guda biyu zuwa biyar su suke samar abin da ake kira baiti. Ƙarshen kowane ɗango (layi) na kowane baiti akan so ya ƙare da sauti iri ɗaya, wannan shi ake kira amsa amo ko kuma ƙafiya. Kenan, salon rubuta waƙa ya bambanta da yadda ake rubutun zube da kuma wasan kwaikwayo. Saboda haka a fagen nazarin waƙa idan aka yi maganar zubi ko salo, to ana son manazarci ya lura da yadda mawaƙi ya buɗe waƙarsa. Yawancin waƙoƙin Hausa, mabuɗinsu shi ne addu’a. Misali, idan muka duba baitoci biyun farko na waƙar  ‘Maraba da Soja’ ta malam Sa’adu Zungur:

  Mu yi salati da sallamawa,
  Ga fiyayyen Annabawa,
  Wanda ya shige kwaikwayawa,
  Shugaban duka jarumawa,
  A gare shi mu ke biɗar fakewa.

  Allah ɗai ad da ƙudura,
  Mulki, iko, da nasara,
  Babu tasiri da sutura,
  Ba tsimi, kuma ba dabara,
  Sai da ƙarfin Jalla, Mai iyawa.

  Idan muka lura za mu taras cewa baitin farko ya fara ne da salati ga Annabi da kuma yabo gare shi. Sannan kuma sai yabo ga Allah wanda ke ƙunshe da sallamawar dukkan al’amura gare shi kuma hakan na nufin neman taimakonsa a cikin dukkan al’amura kamar yadda ya zo a biti na biyu. To, wannan nau’i ne na addu’a a waƙa.

  Bayan wannan kuma sai ƙarshen waƙar, marufi kenan. Shima abin dubawa ne. Wasu sukan rufe waƙoƙinsu da addu’a, wasu kuma da bayyana adireshinsu, wasu kuma sukan haɗe biyun. Misali, Na’ibi Sulaimanu Wali, ya rufe waƙarsa ta Hawainiya da addu’a da kuma faɗin adireshinsa kamar haka:

  Na gode Allah nai yabo,
                 A gare shi a nan zan dakata.

  Tsira da amincin Rabbana,
                Ga Rasulu da ya hana yin fuce.

  Ko za a cane maka wa ya yi?
                Waƙan nan malam sai ka ce.

  Na’ibi Wali sunansa ne,
                 Kuma Kurawa unguwarsu ce.

  Tamat, yau waƙata ta cika,
                Allah sa mu mu bar son yin fuce.

  Bayan an nazarci mabuɗi da marufin waƙa kuma sai a koma baitocinta, a nan kuma za a lura da ɗangwayen waƙar (layuka), an zuba ta  a baituka biyu-biyu ne, uku-uku, hur-huɗu ne, ko biyar-biyar? Ba za a so samun saɓani wajen adadin ɗangwayen da ke samar da baitukan waƙar ba. Sai kuma ƙafiya wato amsa amo, shima an fi so ya zama abu guda tun daga farko har ƙarshen baiti. Idan aka lura da waƙar Maraba da Soja ta Malam Sa’adu Zungur, za a ga  cewa a baitin farko, dukkanin ɗangwayen suna ƙarewa ne da sautin wa.

 3. Salon Sarrafa Harshe: Salon sarrafa harshe na nufin irin Hausar da aka yi amfani da ita wajen rubuta waƙa, da kuma shigo da adon harshe cikin waƙar ta hanyar karin magana, kirari, habaici, kamantawa da sauransu. Yin amfani da sauƙaƙƙiya kuma daidaitaciyyar Hausa shi aka fi so, don waɗannan su za su saka waƙar ta zamo mai sauƙin fahimta da kuma daɗin karantawa ga mai karantata.

Bin waɗannan matakai, shi ne zai baiwa manazarci damar sanin in da akalar waƙa ta saka gaba har ya gane saƙon da ke cikin waƙa idan abar lura ce, ko kuma yin kullaliyo da ita da kuma bata sunan da ya dace da ita amma ba waƙe ba.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zungur A. M. S. (1968). Waƙoƙin Sa’adu Zungur. The Northen Nigerian Publishing Company Ltd, Zariya – Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub