Sadarwa: Amfani da Alamomi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Amfani da Alamomi


Gabatarwa

Amfani da alamomi tsohuwar, daɗaɗɗiyar hanyar sadarwa ce a wajen Bahaushe tun kafin gaurayuwarsa da kowace baƙuwar fuska.

Ta wannan siga Bahaushe yana amfani da zane-zane, zanen suna, zanen fuska da kuma sana’ar fiƙe da sassaƙa wajen sadarwa.

Zane-zane

A gargajiyance, a zamanin baya, fatake suna da alamomin da suka keɓanta da kowane daga cikinsu, da suke zanawa a jikin dabbobinsu. Idan masu korar dabbobi suka kora aka kai kasuwa, koda mai kayan bai je kasuwa ba, to za a ware nasa a bai wa dillalinsa ya sayar masa. Haka nan kuma koda a zaman gida, idan dabbar wani ta shiga cikin ayarin wasu dabbobin a wajen kiwo har ta kai ga ta shiga gidan wani, da zarar magariba ta ƙarato, to idan aka ga wannan baƙuwar dabba, abin yi kawai shi ne za a duba zanen jikinta, da zarar an ga zanen, to an san gidan da ta fito, sai a bai wa yaro ya ja ya kai gidan masu ita.

Zanen Suna

Tun kafin kowane baƙo ya zo ƙasar Hausa, Bahaushe yana da hanya da yake bi wajen raɗa wa jariri ko jaririya suna. Ana samun siyaye; wato karan rama, a ɓara shi ko a tsaga shi gida biyu, sai a samu guda bakwai a zazzana alamomi daban-daban a jiki, sai a kai wa mai jego ta zaɓi guda a ranar suna. Dukkan wanda ta zaɓa a ciki, sai a dawo da shi zuwa ga dattawan da tun asali su suka zana waɗannan alamomi, da sun ga wanda mai jegon ta zaɓa, to sai su yi amfani da alamar da ke jikin wannan siyaye da mai jego ta zaɓa su ambata sunan abin haihuwa.

Dan gane da wannan magana, ga wani abu da zan ce da ku wanda na jiyo daga Farfesa Bunza (2002), domin guiwarku ta yi ƙarfi, “Ganin haka, masana Hausa ke ganin dole, akwai hanyar sadarwar rubuce a Hausa ta gargajiya”.

Zanen Fuska

Zanen fuska, tsohuwar al’ada ce ta sadarwar Bahaushe. Ta wannan hanya Bahaushe yake faɗin irin yankin da ya fito da kuma irin sana’ar gidansu a Ƙasar Hausa.

Misali, akwai zanen fuska da ya yi fice da sunan ‘Yar Katsina a Ƙasar Hausa. Sannan kuma akwai wani na’u’in bille (zanen fuska ne) da ake yi a ɓarin dama na fuskar mutum wanda mahauta suka keɓanta da shi a Ƙasar Hausa. Idan da za ka ga mutum da ‘Yar Katsina a fuskarsa, kuma ga bille a ɓarin dama na fuskarsa, to wannan mutum yana gaya maka cewa, ni mutumin ƙasar Katsina ne kuma sana’ar gidanmu ita ce fawa. Ko kuma kai tsaye yana cewa da kai, ni mutumin Katsina ne kuma mahauci ba tare da ka ji furuci daga bakinsa ba.

Feƙe da Sassaƙa

Waɗannan sana’o’i ne na gargajiyar Bahaushe, waɗanda ke cike da hikima da dabarar isar da saƙo. Waɗannan masu sana’a suna yin zane-zane ne a jikin kayan amfanin gida da sauransu. Suna zana alamomi a jikin akushi, ludayi, butar duma, mafici, ƙwarya da sauransu. Ta irin wannan hanya suke bambanta ludayi, ƙoƙon-sha da kuma butar mai gida. Duk wanda ya ga wannan alama a jikin waɗannan abubuwa da aka lissafa, to ya san cewa wannan buta, ludayi ko ƙoƙo na mai gida ne, saboda haka ba zai yi wasa da shi ba. Kuma haka abin yake a fannin saƙar tabarma, mafici, malafa, da sauransu.

Idan muka waiwaici Farfesa Bunza (2006), kan wannan magana, za mu ji shi yana cewa: “Daga cikin sana’o’in akwai basira da hikima da suka nuna akwai dabarar sadarwa ta gargajiya a ciki”.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub