Sadarwa: Amfani da Baki

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Amfani da Baki


Gabatarwa

Ana amfan da baki wajen isar da saƙonni da dama. Daga ciki akwai:

  1. Murguɗa Baki: Alama ce ta raini
  2. Zumɓura Baki: Idan yaro ya zumɓura baki, wannan na nuna shagwaɓa, idan kuma babban mutum ne ya yi, to wannan na nufin raini ne.
  3. Buɗe Baki: Alama ce ta mamaki. Bahaushe kan hangame bakinsa domin nuna mamakin faruwa ko ganin wani abu.
  4. Gwalo: Gwalo shi ne zare idanu tare da harshe a lokaci guda. Gwalo kuwa alama ce ta nuna raini.
  5. Murmushi: Murmushi alama ce ta soyayya.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub