Sadarwa: Amfani da Hannu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Amfani da Hannu


Gabatarwa

Ana amfani da hannu wajen isar da saƙonni da dama da suka haɗa da gaisuwar ban-girma, gargaɗi, amincewa, kira, tuhuma, kore abu da sauransu.

 1. Gaisuwa: Idan Bahaushe ya dunƙule yatsunsa ya ɗaga hannu sama, ya jijjina, to yana nufin gaisuwa tare da girmamawa. Mutane masu alfarma ake yi wa irin wannan gaisuwa kamar sarakuna da sauransu.
 2. Fatan Alheri: Idan Bahaushe ya ɗaga hannunsa sama, sannan ya saki yatsunsa biyar, ya kaɗa hannun daga dama zuwa hagu, to yana nufin yana yi maka fatan alheri, kamar a ce a dawo lafiya.
 3. Kira: Bahaushe yana amfani da hannun wajen kira. Idan Bahaushe ya miƙar da yatsunsa biyar a haɗe, sannan ya riƙa yafato iska, to yana nufin mutumin da yake nesa da shi ya zo.
 4. Kora: Idan Bahaushe ya miƙar da hannunsa, sannan kuma ya riƙa yarfar da hannun daga ƙasa zuwa sama, to wannan yana nufin a tafi a bashi guri; wato dai, yana korarka ne daga wurin.
 5. Jin Zafi/Ciwo: Idan Bahaushe ya riƙa yarfar da hannunsa ba ƙaƙƙautawa, wannan yana nuna cewa yana jin raɗaɗi.
 6. Gargaɗi: Idan Bahaushe ya miƙar da ɗan yatsansa (Manuni), sannan ya dunƙule sauran guda huɗun, sai kuma ya riƙa karkaɗa yatsan dake miƙe, to yana ja maka kunne kenan.
 7. Zagi: Idan Bahaushe ya ɗaga tafin hannunsa ya nuna maka, sannan kuma yatsunsa biyar a ware, to yana zagi kenan. Wannan shi ake kira daƙuwa.
 8. Godiya/Sannu: Idan Bahaushe ya miƙar da tafukansa biyu yana bubbuga su a hankali kamar yana tafi, to yana nufin ya gode, ko sannu ko kuma babu komai ko muna tare. Amma shi muna tare haɗe su ake yi na na ɗan lokaci.
 9. Zagin Ƙasƙanci: Idan Bahaushe ya miƙar da yatsunsa alhali suna jere da juna, sannan ya riƙa kaɗa hannun daga dama zuwa hagu, to yana nufin mutum bashi da hankali.
 10.  Ƙirga: Bahaushe yana nuna yatsa a maimakon adadi. Misali, yatsa ɗaya ga lamba ɗaya, yatsu biyu lamba biyu, haka-haka. Idan kuma Bahaushe ya kaikaita tafin hannunsa, yatsun a miƙe sannan ya giciya shi a tsakiyar ɗayan to wannan yana nufin rabi.
 11.  Yanka: Idan Bahaushe ya miƙar da tafin hannunsa, sannan ya giciya shi a maƙogwaronsa kuma a kaikaice, to yana nufin yanka.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub